A cikin shirinmu na farko, za mu bayyana muku wasu labarun da ke da nasaba da kabilu daban-daban na kasar Sin. Da farko dai, ga labaru 2 game da yadda kasar Sin ke raya harufai da kalmomin kabilunta daban-daban.
Labarin farko shi ne, gwamnatin kasar Sin ta bai wa kananan kabilu taimako wajen kirkira da kyautata haruffa da kalmominsu.
Gwamnatin kasar Sin tana fatan ba ma kawai kowace kabila tana da yarenta ba, har ma tana da haruffa da kalmominta. Sabo da haha, tun daga shekarar 1949, wato lokacin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, gwamnatin kasar Sin ta ba da taimako ga kabilu masu dimbin yawa ciki har da kabilun Zhuang da Dai wajen kirkiro da kyautata haruffa da kalmominsu.
Kasar Sin tana da kananan kabilu 55. Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, yawancin kabilu suna da yarensu, amma ban da kabilun Hui da She da Man wadanda suka yi amfani da harshen Sinanci, kabilu 18 ciki har da Mongoliya da Uygur da Tibet kawai ne suke da haruffa da kalmominsu. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekarar 1949, gwamnatin kasar Sin ta aika masana wadanda suka kware kan haruffa da kalmomi zuwa yankunan da 'yan kananan kabilu suke zama domin binciken halin haruffa da kalmomin kananan kabilu suke ciki. Bisa tushen wannan bincike da ka'idojin "yin zabe da kansu" da yin kyakkywan tasiri wajen raya kabilu daban-daban, masana sun taimaki kananan kabilu fiye da 10 ciki har da kabilun Zhuang da Miao wajen kirkiro haruffansu bisa harufan Latin. Sannan sun taimaki kabilun Dai da Lahu wajen kyautata harufansu.
Labari daban shi ne kasar Sin ta kara saurin shigar da haruffa da kalmomin kananan kabilunta cikin injuna masu kwakwalwa.
Tun daga shekaru 80 na karnin da ya gabata ne kasar Sin ta soma aikin nazarin yadda za a iya shigar da haruffa da kalmomin kananan kabilunta cikin injuna masu kwakwalwa. A cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, an samu ci gaba kan wannan aiki. Ya zuwa yanzu, an riga an tsara ma'aunin da ke matsayin kasar game da hanyar shigar da haruffa da kalmomi na Mongoliya da Tibet da Uygur da Khazak da Kirkiz da Koriya da Yi da Dai a cikin injuna masu kwakwalwa. Kasashen duniya suna amincewa da wannan ma'aunin da kasar Sin ta tsara. Yanzu ana iya amfani da manhajar da ke dauke da harufai da kalmomin kananan kabilun kasar Sin a kan tsarin Windows. (Sanusi Chen)
|