Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-24 18:07:30    
An yi bikin murnar cikon shekaru 10 da jibge rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin a Hong Kong a yau

cri

Ran 24 ga wata, a sansanin rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, an yi babban taron murnar cikon shekaru 10 da jibge rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin a Hong Kong.

A gun babban taron, janar Ge Zhenfeng mataimakin hafsan hafsoshin rundunar 'yantar da jama'ar Sin ya yi jawabin cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, bayan da ake jibge rundunar 'yantar da jama'ar Sin a Hong Kong a Hong Kong, rundunar tana bin ka'idar 'kasa daya amma tsarin mulki 2' a tsanake, tana kuma tafiyar da harkokin soja da kuma tsaron Hong Kong bisa shari'a. Sa'an nan kuma, tana goyon bayan hukumar yankin musamman na Hong Kong wajen aiwatar da manufofi bisa dokoki, da kuma shiga harkokin jin dadin jama'a cikin himma da kwazo. Rundunar nan ta ba da gudummowarta wajen tabbatar da samun wadata da kwanciyar hankali da kuma bunkasuwa yadda ya kamata a Hong Kong.

Dadin dadawa, gwamnan hukumar yankin musamman na Hong Kong Donald Tsang ya bayyana cewa, a cikin wadannan shekaru 10 da suka wuce, rundunar 'yantar da jama'ar Sin ta samar da kyakkyawar siffa a zukatan jama'ar Hong Kong a sakamakon ayyukan da suka yi. Ayyukan da ta yi sun kyautata tunanin jama'ar Hong Kong ta fuskar kasancewa a matsayin mutanen Sin, jama'ar Hong Kong sun kara sanin cewa, Hong Kong wani bangare ne na mahaifiyarmu kasar Sin.(Tasallah)