Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-22 21:51:55    
Tsarin "kasa daya amma tsarin mulki biyu" yana gudana yadda ya kamata bayan da aka maido da Hongkong a karkashin mulkin Sin

cri
Wani rahoton shekara shekara na kwamitin kungiyar tarayyar Turai ya bayar a yau dangane da Hongkong ya yi nuni da cewa, tun bayan da Sin ta maido da mulkinta a Hongkong a shekarar 1997, an nuna girmamawa ga ka'idar "kasa daya amma tsarin mulki guda biyu", kuma tsarin yana gudana yadda ya kamata.

Rahoton ya yi nuni da cewa, gwamnatin yankin musamman na Hongkong tana ci gaba da samun 'yancin cin gashin kanta sosai a fannonin tattalin arziki da ciniki da kudi da dai sauransu, kuma mazaunan Hongkong ma sun ci gajiyar tsarin doka da ikon mallakar kayayyaki da 'yancin fadin albarkacin bakinsu da kuma tsarin tattalin arzikin kasuwanci na Hongkong.

Rahoton ya kuma kara da cewa, tun daga shekarar 1997, huldar da ke tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Hongkong ta ci gaba da bunkasa, yanzu kungiyar tarayyar Turai ta riga ta zama babbar abokiyar ciniki ta biyu ta Hongkong, wato bayan babban yankin kasar Sin.(Lubabatu)