Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-22 17:26:49    
Kasar Amurka na gaggauta warware batun nukiliyar Korea ta Arewa

cri

An labarta cewa, jagoran tawagar wakilan kasar Amurka a gun shawarwari tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa bugu da kari mai bada taimako ga sakatariyar harkokin wajen kasar, Mr. Christopher Hill ya kai ziyarar ba zata jiya Alhamis a Korea ta Arewa, wato ke nan ya kasance wani babban jami'I na farko na kasar Amurka da ya kai ziyara a Phongyang tun shekaru biyar da suka gabata. Wannan dai ya alamanta cewa, kasar Amurka ta rigaya ta canza matsayin da ta dauka na rashin yin tuntubar Korea ta Arewa, hakan ya shaida cewa, kasar Amurka za ta gaggauta warware batun nukiliyar Korea ta Arewa.

Lallai ba a manta ba , tuni lokacin da Mr. Bill Clinton ke rike da mulkin kasar Amurka, ya taba tura tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Madam Madeleine K. Albright zuwa Korea ta Arewa domin yin ziyara. Amma tun bayan da Mr. Bush ya hawa kan kujerar mulkin kasar, sai gwamnatin Amurka ta nuna tsattsauran ra'ayi game da harkokin Korea ta Arewa. Kafofin yada labarai na kasar Amurka sun bayar da labarin, cewa bayan da Mr. Hill ya zama jagoran tawagar wakilan Amurka a gun shawarwarin tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa, har kullum yakan yi kokarin daba yiwuwar kai ziyara a Korea ta Arewa. Mr. Hill ya bayyana ra'ayinsa, cewa yin cudanya da bangaren Korea ta Arewa kai tsaye zai iya kara fahimtar tunanin gwamnatin Korea ta Arewa; haka kuma zai taka rawa wajen daukaka ci gaban shawarwarin tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa. Saukar Mr. Hill ke da wuya a Pyongyang, sai nan da nan ya jaddada cewa ya kamata a ci gaba da gundanar da yunkurin shawarwarin tsakanin bangarori shida a maimakon bata lokaci da yawa kamar yadda aka yi a da.

A ran 13 ga watan Fabrairu na wannan shekara, a zauren taron shawarwarin tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa, an zartar da wata takardar hadin gwiwa ta " Matakin farko na aiwatar da sanarwar hadin gwiwa", inda aka tanadi cewa, ya kamata gwamnatin Korea ta Arewa ta rufe tashoshinta na nukiliya a Yongbyong, da gayyatar sufetocin hukumar kula da makamashi ta duniya don su sake koma wa Korea ta Arewa; kuma ya kamata sauran sassa daban-daban su bai wa Korea ta Arewa gudummowar makamashi cikin gaggawa; A yadda wannan takardar hadin gwiwa ta tanada, an ce, kamata ya yi bangarori daban-daban su soma aiwatar da wadannan kudurori cikin kwanaki 60. Amma an ga tilas ne a dage lokacin aiwatar da wadannan kudurori saboda cikin dogon lokaci ne ba a warware maganar janye haramcin da aka sanya wa Korea ta Arewa wajen yin amfani da kudadenta da yawansu ya kai dolar Amurka miliyan ashirin da biyar da ta ajiye a Bankin Delta Asiya ba. Sai dai a ran 18 ga wata ne aka yi shelar daidaita wannan magana. Kafin wannan, ma'aikatar harkokin waje ta Korea ta Arewa ta bayyana cewa, da zarar an warware wannan magana, sai nan da nan za ta rufe tashoshinta na nukiliya a Yongbyong, da aike da goron gayyata ga sufetocin hukumar kula da makamashi ta duniya don su kai ziyara da kuma yin shawarwari sosai tare da kasar Amurka kan yadda za a aiwatar da matakan nan gaba bayan rufe tashoshinta na nukiliya.

A nata bangaren, hukumar kula da makamashi ta duniya ita ma ta shelanta, cewa wata tawagar wakilanta dake kunshe da manyan jami'ai za ta kai ziyara a Korea ta Arewa a ran 25 ga wata bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi mata.

Kafofin watsa labarai na Amurka sun kiyasta, cewa wani muhimmin dalilin da ya sa gwamnatin Amurka ta gaggauta warware batun nukiliyar Korea ta Arewa, shi ne domin a halin yanzu kasar Amurka na fuskantar matsaloli da dama game da harkokin waje, ciki har da batutuwan Iraki da Iran. Lallai gwamnatin Amurka tana neman cimma tudun dafawa wajen daidaita wadannan batutuwa. Daidai bisa wannan yanayi ne, Mr. Bush wanda wa'adin aikinsa shekara daya da 'yan watanni ne kawai da ya rage na bukatar shaida wa bainal jama'ar kasar Amurka cewa, za su iya kawar da a kalla " barazana" daya da take fuskanta, wato batun nukiliyar Zirin Korea.

Bisa labarin da muka samu, an ce, Mr. Hill ya sa ran alheri ga maido da shawarwarin tsakanin bangarori shida kan batun nukiliyar Korea ta Arewa da za a gudanar a wata mai kamawa. Amma duk da haka, wasu manazarta sun bayyana shakkunsu kan shin ko za a iya samun ci gaba da sauri a gun shawarwarin kamar yadda gwamnatin Amurka take kyautata zato a kai. (Sani Wang )