Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-20 15:21:49    
Kasar Sin ta sa himma ga hada guiwar tsakaninta da kasashen duniya don kiyaye kayayyakin tarihi na al'adunta

cri

Kasar Sin tana da dogon tarihi tare da dimbin al'adu. Kabilunta 56 suna da halayensu na musamman sosai wajen al'adu, don kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu masu daraja sosai da kakani-kakanin kasar Sin suka bari, gwamnatin kasar Sin ta riga ta ba da iznin daddale yarjejeniyoyin kasashen duniya da yawa don kiyaye al'adu, kuma ta yi hadin guiwa da kungiyoyin kasa da kasa sosai don aiwatar da harkokin kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu.

A shekarar 1985, kasar Sin ta ba da iznin shiga yarjejeniyar kiyaye al'adu da kayayyakin tarihi na hallitu na duniya, a shekarar 1987, an mayar da tsohuwar fadar sarakuna wato Gugong da babbar ganuwar kasar Sin cikin littafin tanadin sunayen kayayyakin tarihi na duniya. Sa'anan kuma, aikin kasar Sin na neman shiga jerin kayayyakin tarihi na al'adun duniya yana kara saurinsa, ya zuwa watan Yuli na shekarar da ta shige, da akwai kayayyakin tarihi na al'adu da na hallitu da yawansu ya kai 33 na kasar Sin da suka shiga jerin kayayyakin tarihi na al'adun duniya, yawansu ya kai matsayi na uku a duniya.

Shugaban cibiyar kula da harkokin kayayyakin tarihi ta duniya Mr Francesco Bandarin ya kawo ziyara a kasar Sin ba sau daya ba ba sau biyu ba, ya bayyana cewa, kasar Sin ta sami sakamako wajen kiyaye kayayyakin tarihi, ya ce, zuwa kasar Sin na da muhimmanci sosai, kasar Sin tana da wadatattun albarkatan kayayyakin tarihi na al'adu da na halittu , yanzu ta zama kasa ta uku da ke tanadin kayayyakin tarihi. A cikin shekaru 20 da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai masu kyau sosai don kada a lalata kayayyakin tarihi, kuma gwamnatin ta lura sosai kan darajar kayayyakin tarihi da ke da muhimmanci ga zuri'armu.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, an kira taruruka da yawa masu muhimmanci sosai kan kiyaye kayayyakin tarihi a kasar Sin, wasu kungiyoyin kiyaye kayayyakin tarihi na kasshen duniya su ma sun kafa kananan hukumominsu a kasar Sin.

Mataimakin shugaban hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na kasar Sin Mr Zhang Bai ya bayyana cewa, cibiyar kiyaye kayayyakin tarihi ta birnin Xi'an ita ce reshin farko da majalisar kiyaye kayayyakin tarihi ta duniya ta kafa a duniya, an kafa ta a kasar Sin, wannan ya bayyana cewa, kungiyar kasashen duniya ta amince da kasar Sin. Ya ce,

lokacin da aka soma kafawa, wasu kasashe suna da bambancin ra'ayi, amma a karshe dai, an tabbatar da wannan batu, wato an kafa cibiyar a kasar Sin, wannan ya shaida cewa, hadin guiwar da ke tsakaninmu sai kara yawa yake yi, kuma ya bayyana cewa, hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na kasa da kasa sun amince da kasar Sin wajen ayyukan kiyaye kayayyakin tarihi, kuma sun mai da muhimmanci ga kasar Sin, matsayin da kasar Sin take tsayawa ya sami sauyawa sosai a duniya.

Kasar Sin ita ma ta yi amfani da fasahohin kasashen waje wajen kiyaye kayayykin tarihi , kuma hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na kasar Sin tana yin hadin guiwa a tsakaninta da kasashen waje cikin dogon lokaci tare da samun sakamako da yawa. Mataimakin shugaban hukumar kiyaye kayayyakin tarihi na kasar Sin Mr Zhang Bai ya bayyana cewa, hadin guiwar da ke tsakanin gwamnatin Sin da kungiyoyin kiyaye kayayyakin tarihi na kasashen duniya da kuma tsakanin kungiyoyin da ba na gwamnati ba a fannoni da yawa sai kara yawa ake yi, a wajenmu, mun sami fa'ida mai tsoka, kuma muna amfnai da sakamakon da aka samu wajen yin hadin guiwar, a cikin hadin guiwar, mun yada fasahar gargajiyarmu gare su, saboda haka, wannan shi ne karin taimako da aka samar wa junansu, a gaskiya dai mun sami babbar fa'ida.(Halima)