Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-20 15:13:12    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(14/06-20/06)

cri
Ran 17 ga wata, a cikin karon karshe na gasa tsakanin kungiya kungiya domin cin kofin Sudirman na wasan kwallon badminton ta karo na 10 da aka yi a birnin Glasgow na kasar Birtaniya, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Indonesia da ci 3 ba ko daya, ta sake zama zakara a gun gasar. Wannan ne karo na 6 da kungiyar Sin ta ci kofin Sudirman. Gasar cin kofin Sudirman ta wasan kwallon badminton na daya daga cikin gasanni mafiya nagarta na wasan kwallon badminton na duniya, inda 'yan wasa maza da mata suka kafa wata kungiya don yin takara da juna. An bude gasa ta wannan karo ne a ran 11 ga wata, inda kungiyoyi 16 suka kara da juna. Za a yi gasa ta karo na 11 a birnin Guangzhou na kasar Sin a shekarar 2009.

Ran 18 ga wata, a nan Beijing, an kaddamar da daukar masu aikin sa kai na birnin na taron wasannin Olympic na Beijing da taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing. A gun bikin kaddamar da wannan aiki, wani jami'in kungiyar kula da masu aikin sa kai ta taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, an yi shirin daukar masu aikin sa kai dubu dari 4 daga 'yan birnin Beijing da suka lakanci wannan birni sosai, wadanda za su yi aikin sa kai domin tabbatar da gudanar da gasanni da kuma tafiyar da harkokin birnin yadda ya kamata a wajen filayen wasa da kuma sauran muhimman wuraren birnin a lokacin da ake yin wadannan tarurukan wasannin motsa jiki 2 a shekara mai zuwa. Za a kammala wannan aiki a watan Yuli na shekara ta 2008.

Akwai wani labari daban game da tawon wasannin Olympic na Beijng, an ce, a kwanan baya, wani jami'in kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya fayyace cewa, a lokacin da ake yin taron wasannin Olympic na Beijing, za a yi amfani da motoci fiye da dubu 5 domin gasanni. Za a kammala kafa wannan babban ayarin motoci a watan Yuni na shekara mai zuwa. Motocin za su ba da hidimomi ga jami'ai da 'yan wasa da manema labaru daga duk duniya a lokacin gasar.

A ran 15 ga wata, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta gabatar da sabuwar takardar jerin sunayen kungiyoyin wasan kwallon kafa na mata, inda kasar Amurka ta ci gaba da zama ta farko, kasar Sin kuwa ta ci gaba da zama ta 11. Kasashen Jamus da Sweden da Norway da Korea ta Arewa da Denmark da Faransa da Brazil da Canada da kuma Japan sun zama ta 2 zuwa ta 10.(Tasallah)