Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 21:55:08    
Shugaban AU ya yi kira a aiwatar da yarjejeniyoyin da ke shafar batun Darfur

cri

Ran 18 ga wata, a babban zauren Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU, shugaba Alpha Oumar Konare na kwamitin kungiyar AU ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya su hada kansu wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da bangarorin da abin ya shafa suka daddale domin daidaita batun Darfur, ta haka za a sa kaimi kan warware wannan batu ta hanyar siyasa.

A lokacin da yake yin shawarwari da wakilin musamman na kasar Sin Liu Guijin, wanda ke kula da batun Darfur, Mr. Konare ya bayyana cewa, yanzu an sami ci gaba mai yakini a fannin daidaita batun Darfur, shi ya sa bai kamata ba a ci gaba da matsa wa gwamnatin kasar Sudan matsin lamba. Ya kamata kasashen duniya su dora muhimmanci kan aiwatar da yarjejeniyoyin da abin ya shafa da kuma sa kaimi ga gwamnatin Sudan da ta ci gaba da yin hadin gwiwa da kasahen duniya.

Ya kara da cewa, nada wakilin musamman mai kula da batun Darfur da gwamnatin Sin ta yi muhimmin mataki ne da ta dauka. Kungiyar AU ta nuna wa kasar Sin yabo saboda muhimmiyar rawa da take takawa kan warware batun Darfur.

A nasa bangaren kuma, Mr. Liu ya ce, bayan da ta yi tattaunawa da shawarwari da kungiyar AU da Majalisar Dinkin Duniya, gwamnatin Sudan ta sanar da amincewa da girke hadaddun sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisa Dinkin Duniya da kungiyar AU a yankin Darfur, kasar Sin ta yi maraba da wannan. Sa'an nan kuma, a nan gaba kasar Sin za ta kara goyon bayan kokarin da kungiyar AU ke yi, za ta zabura wajen daidaita batun Darfur yadda ya kamata tun da wuri.(Tasallah)