Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 20:35:51    
Kasar Sin ta yi kokarinta kan kyautata halin da shiyyar Darfur ke ciki

cri
Yau 19 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Qin Gang ya ce, kasar Sin ta yi kokari sosai a fannonin tabbatar da zaman lafiyar shiyyar Darfur ta kasar Sudan, da kuma kyautata halin kwanciyar hankali da na jin kai da shiyyar ke ciki.

A gun taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Mr. Qin Gang ya ce, kasar Sin na kula da batun Darfur kamar sauran kasashen duniya, tana fatan sassauta halin jin kai mai tsanani da ake ciki a shiyyar Darfur da sauri, kazalika tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su yi shawarwari, domin gano bakin zaren warware matsalar kamar yadda ya kamata. A waje daya kuma, kasar Sin na tsayawa kan matsayin girmama gwamnatin Sudan, a lokacin da ake neman hanyar warware matsalar. (Bilkisu)