Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-19 15:31:41    
Yin amfani da wayar salula cikin dogon lokaci ya kara barazanar kamuwa da ciwon sankarar kwakwalwa

cri

Masu ilmin kimiyya sun sha yin rikici kan mene ne tasirin da yin amfani da wayar salula da kuma wayar tarho ba tare da waya ba cikin dogon lokaci ya kawo wa mutane. A kwanan baya, wata hukumar nazari ta kasar Sweden ta ba da sakamakon nazari cewa, yin amfani da wayar salula cikin dogon lokaci ya kara kawo wa mutane barazanar kamuwa da ciwon sankarar kwakwalwa.

A cikin wani rahoton da cibiyar nazarin tsawon ran aiki ta kasar Sweden ta bayar, an ce, cibiyar nan ta zabi masu fama da ciwon sankara 2200, a sa'i daya kuma, ta zabi mutane masu koshin lafiya 2200, daga baya, ta yi bincike da kwatanta halin da suke ciki wajen yin amfani da wayar salula da wayar tarho ba tare da waya ba. Sakamakon bincike ya shaida cewa, yin amfani da wayar salula ko kuma wayar tarhi ba tare da waya ba kullun ya kara kawo wa mutane barazanar kamuwa da ciwon sankara a cikin kwakwalwa kwarai.

Ban da wannan kuma, bayan da suka yi nazari, masu ilmin kimiyya sun gano cewa, idan wani mutum ya fi amsa wayar salula da kansa na hagu, to, kwakwalwarsa ta hagu za ta kara samun hadari, wannan mutum zai kara samun barazanar kamuwa da ciwon sankara a cikin kwakwalwarsa ta hagu. Mai kula da wannan aiki ya bayyana cewa, idan wani mutum ya yi amfani da wayar salula har tsawon awoyi 2000 a duk ransa, to, yawan kamuwa da ciwon sankara a cikin kwakwalwa ta hagu ko ta dama da ya fi yin amfani da shi wajen amsa waya ya karu da sau 2.4, in an kwatanta da sauran mutane, hanyar da za a bi don magancen wannan barazana ita ce yin amfani da belun kunne a maimakon amsa wayar salula kai tsaye.

Wannan jami'i ya kara da cewa, nazarin da aka yi a wannan gami nazari ne da aka fi yin bincike kan mutane masu yawa, kuma an dade ana yin wannan nazari, in an kwatanta shi da sauran irin wannan nazari. An kuma yi la'akari da al'adun shan taba da tarihin aiki da kuma ko ya yi aiki ko ya zama kusa da kayayyakin da ke jawo wa mutane illa ko a'a.(Kande)