A ran 18 ga wata, a birnin Beijing, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya bayyana cewa, kasar Sin ta raya dangantakar da ke tsakaninta da Afirka ne domin samun ci gaba da bunkasuwa gaba daya bisa tushen nuna sahihanci da sada zumunta da zaman daidai wa daida don moriyar juna a maimakon neman samun moriya don kanta kawai.
Lokacin da Mr. Yang ke halartar liyafar dare da kungiyar jakadun kasashen Afirka da ke kasar Sin ta shirya bisa gayyatar da aka yi masa, ya ruwaito babban ci gaba da dangantaka a tsakanin Sin da Afirka ta samu a 'yan shekarun nan da suka gabata, kuma ya yi bayani kan yadda ake aiwatar da sakamako mai kyau da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Ban da wannan kuma ya ce, kara inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wani muhimmin abu ne da ke cikin manufofin diplomasiyya da kasar Sin ke bi wajen samun 'yancin kai ba tare da tsangwama ba da kuma zaman lafiya, haka kuma zabi ne da kasar Sin ta yi wajen bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana da sa kaimi ga raya duniya mai jituwa. Kasar Sin za ta dora muhimmanci kan raya dangantakar hadin kai da aminci tsakaninta da kasashen Afirka kamar yadda take yi kullum domin zama aminiyar jama'ar Afirka har abada.(Kande Gao)
|