A ran 18 ga wata, firayim ministan karar Habasha Meles Zenawi ya bayyana cewa, ya kamata kungiyar tarrayar Afirka wato AU da MDD su bayar da gudummowar jagoranci kan batun Darfur na kasar Sudan, da kuma warware batun Darfur ta hanyar siyasa bisa shawarwarin da AU da MDD da gwamnatin kasar Sudan suka yi.
Lokacin da Mr. Meles ke yin shawarwari tare da Liu Guijin, manzon musamman na gwamnatin kasar Sin kan batun Darfur, ya ce, bisa matsayinta na wata membar kungiyar AU da wata kasa aminiya da ke makwabtaka da kasar Sudan, kasar Habasha tana fatan za a iya warware batun Darfur tun da wuri, wanda zai ba da taimako wajen kiyaye ikon mulkin kan kasar Sudan da cikakken yankin kasar, da kuma samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar, haka kuma zai ba da taimako wajen sa kaimi ga shimfida zaman lafiya a tsakanin shiyyar da ke arewacin kasar Sudan da na kudancin kasar.
Bugu da kari kuma Mr. Meles ya nuna yabo sosai ga kasar Sin da gudummowa mai muhimmanci da ta bayar kan batun Darfur da kuma kokarin da ta yi wajen warware batun tun da wuri.(Kande Gao)
|