Ran 18 ga wata, an tsai da kuduri kan batutuwan kasar Uganda da yankin Darfur da sauran batutuwa a gun taron ministocin harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai wato EU da ake yi a kasar Luxembourg.
Bisa abubuwan da ke cikin kuduri game da batun kasar Uganda, an ce, kungiyar EU ta nanata goyon bayan yin tattaunawa a tsakanin gwamnatin Uganda da kungiyar LRA domin daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Sa'an nan kuma tana son nuna goyon baya ga aikin shimfida zaman lafiya a Uganda, za ta kuma ba da tallafin jin kai. A sa'i daya kuma, tana fatan gwamnatin Uganda za ta hada kanta da kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da abin ya shafa a harkokin jin kai da raya tattalin arziki.
Kazalika kuma, taron ya tsai da kuduri kan batun Darfur, inda kungiyar EU ta yi maraba da cimma daidaito a tsakanin kasar Sudan da Majalisar Dinkin Duniya a fannin ba da sauki wajen gudanar da harkokin jin kai a yankin Darfur, ta kuma yi kira ga bangarori masu gwagwarmaya da juna da su bi yarjejeniyar tsagaita bude wuta don tabbatar da tsaron lafiyar masu ba da agajin jin kai da kuma gudanar da harkokin jin kai yadda ya kamata. Bayan wannan kuma, kudurin ya yi maraba da kudurin da gwamnatin Sudan ta tsai da a kwanan baya, wato Sudan ta amince da jibge hadaddun sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU da Majalisar Dinkin Duniya a Darfur.
Dadin dadawa, an tsai da kuduri kan batutuwan yankin Balkan na yamma da kuma Kosovo a gun wannan taro.
|