Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-18 15:31:19    
Kabilar Dong

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kananan kabilun kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu gabatar muku da bayani kan kabilar Dong ta kasar Sin, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: Sabon zama na 'yan kabilar Buyi da ke gabar kogin Huaxi. To, yanzu ga bayanin.

(An fi samun 'yan kabilar Dong a cikin jihohin Guizhou da Hunan da Guangxi na kasar sin. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Dong ya kai miliyan 2.9. 'yan kabilar Dong suna yin amfani da harshen kabilar. A da kabilar ba ta da harafinta ba, sun yi amfani da harafin sinanci. A cikin shekara ta 1958, an fara kago harafin kabilar Dong bisa tushen harafin Latin.

Bayan kafuwar kasar Sin a cikin shekara ta 1949, bi da bi ne an kafa gudumoni da dama na kabilar Dong a cikin jihohin Guangxi da Hunan da kuma Guizhou. Aiwatar da manufofin gudanar da harkokin kananan kabilu da kansu ta cimma burin 'yan kabilar Dong na samun 'yancin kai. Bi da bi ne wuraren nan masu cin gashin kai sun gama gyare-gyaren demokuradiyya a farkon shekaru 50 na karni na 20. Daga baya kuma an fara ayyukan gina al'ummar gurguzu a wuraren, musamman ma bayan taro na uku na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 11 na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, an yi sauye-sauye sosai a yankin kabilar Dong. Yawan amfanin gona yana ta samun karuwa a ko wace shekara sakamakon yin amfani da sabbin fasahohi wajen aikin noma. Ban da wannan kuma an raya sha'anonin noma da bishiyoyi da makiyaya da kiwon kifi. Kafin kafuwar kasar Sin, layin hanyoyin motoci na yankin kudu maso yammacin jihar Guizhou da 'yan kabilar ke ciki ba kai kilomita 500 ba, amma yanzu, wata hanyar jiragen kasa ta iya isa yankin nan, bugu da kari kuma motoci suna iya isa ko wane kauyuka na yankin ta hanyoyin motoci.

Game da sha'anin ilmi, kafin aka 'yantar da kasar Sin, akwai makaratar sakantare guda a ko wace gunduma ta yankin kabilar Dong, kuma yawan makarantun firamare ba su zarce uku ba a ko wace gunduma. Amma yanzu, kusan dukkan yara suna samun zarafin shiga makarantu, samari masu yawa kuwa sun shiga jami'o'i domin kara ilminsu.