Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-18 15:27:53    
Inganta hadin gwiwa tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan a fannin aikin koyarwa domin musaya basirarsu

cri

Aikin koyarwa yana daya daga cikin muhimman abubuwan da gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan wato babban yankin kasar Sin da kuma lardii Taiwan na Sin suke hadin gwiwa da yin mu'amala a kai. A gun taro na karo na uku na dandalin tattaunawa tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan kan tattalin arziki da cinikayya da kuma al'adu da aka yi a birnin Beijing ba da jimawa ba, kwararru da masanan da suka zo daga gabobin biyu sun tattauna kan ci gaba da sa kaimi ga yin mu'amala da hadin gwiwa tsakaninsu a fannoni aikin koyarwa, kuma sun samu ra'ayoyi bai daya da yawa. Ban da wannan kuma bangaren babban yankin Sin ya sanar da cewa, yana nuna maraba da jami'o'in Taiwan da su zo babban yankin kasar Sin wajen daukar dalibai. Ta haka ana iya ganin cewa, hadin kai da yin mu'amala kan aikin koyarwa wata hanya ce mai kyau ga 'yan uwa na gabobin biyu wajen musaya basirarsu da kuma samun bunkasuwa tare. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan batu.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na lardin Taiwan na kasar Sin ya bayar, an ce, wani sabon binciken da aka gudanar ya nuna cewa, 'yan makarantu sakandare na Taiwan da yawansu ya kai kashi 15 cikin dari suna son su zo babban yankin kasar Sin wajen samun ilmi a jami'o'i. Kuma wasu dalibai sun gaya wa wakilinmu cewa, muhimman dalilan da babban yankin Sin ke jawo hankulansu su ne

"za a ba da taimako wajen samun ra'ayoyin zamani na duniya, kuma za a iya samun zarafofi masu yawa wajen samun bunkasuwa a babban yankin kasar Sin a nan gaba. Shi ya sa neman shiga jami'o'in babban yankin Sin abin share fare ne gare mu."

Amma abin bakin ciki shi ne ba a amince da digirin jami'a na babban yankin kasar Sin a Taiwan ba, shi ya sa daliban Taiwan masu yawa ba su iya cimma burinsu ba.

A gun wannan taron dandalin tattaunawa tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan kan tattalin arziki da cinikayya da kuma al'adu, an yi kira da babbar murya ga hukumar Taiwan da ta amince da digirin jami'a na babban yankin kasar Sin tun da wuri.

Shugaban jami'ar Shih Chien ta Taiwan Zhang Guangzheng yana ganin cewa, idan hukumar Taiwan ta amince da digirin jami'a na babban yankin kasar Sin, to zai kawo wa daliban Taiwan alheri sosai. Kuma ya kara da cewa,

"Muna karfafa zukatan daliban Taiwan wajen zuwa babban yankin kasar Sin don kara ilminsu, ta yadda za a taimaka wa dalibai da masana na Taiwan wajen kara fahimtar babban yankin kasar Sin. Kuma sabo da haka za a kara amincewa da al'adun kasar Sin da kuma kwarewarsu wajen yin tunani da yanke shawara su da kansu."

A 'yan shekarun nan da suka gabata, bangaren babban yankin kasar Sin ya fitar da manufofi a jere ga daliban Taiwan wajen samun ilmi da samun aikin yi. Babban yankin kasar Sin ta riga ta amince da digirin jami'a da hukumar kula da aikin koyarwa ta Taiwan ta zartar. Kuma ana ba da gatanci iri daya ga daliban Taiwan da na babban yankin kasar Sin wajen kudin karatu da na wurin kwana da na tikitin wuraren shan iska da dai sauransu, ban da wannan kuma daliban Taiwan suna da damar samun sukolashif. A cikin shekarar da ta gabata kawai, daliban Taiwan fiye da 1700 sun samun sukolashif da yawansu ya zarce kudin Sin Yuan miliyan 7, wato ke nan ya kai kashi 25 bisa dari cikin dukkan yawan daliban Taiwan da suka zo babban yankin Sin wajen karatu.

Neman shiga makaranta da kuma neman samun aikin yi maganganu biyu ne da ba a iya raba su ba. Yanzu ba a kayyade daliban Taiwan ko kadan wajen neman samun aikin yi a babban yankin kasar Sin. Haka kuma yawan abubuwan jin dadin jama'a yana ta samun karuwa, suna iya samun inshorar zaman al'umma kamar yadda mazaunan babban yankin Sin ke yi.

A gun wannan taron dandali, hukumar kula da albarkatun kwadago ta babban yankin kasar Sin ta sanar da cewa, mazaunan Taiwan suna iya shiga jarrabawa iri 15 a fannoni ilmin akanta da fassarada dai sauransu domin neman samun izni.

Shugaban jami'ar Ming Chuan ta Taiwan Li Quan yana ganin cewa, babban yankin kasar Sin ya riga ya zama wata sabuwar kasuwa ga daliban Taiwan wajen samun aikin yi, sabo da haka, a cikin wannan halin da ake ciki, ya kamata a kara inganta hadin gwiwa tsakanin gabobi biyu na mashigin teku na Taiwan wajen aikin koyarwa. Kuma ya kara da cewa,

"malaman gabobin biyu suna iya bayar da darusa tare, da baiwa dalibai jagoranci tare. Haka kuma suna iya hadin kansu wajen yin nazari, da kuma amince da juna wajen makin da dalibai suka samu. Ban da wannan kuma gabobin biyu suna iya ba da darusa a kasashen waje tare domin yada al'adun kasar Sin a ketare, ta yadda jami'o'in gabobin biyu za su iya kyautata ingancinsu wajen samar da ilmi gaba daya."(Kande Gao)