Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-16 17:59:50    
Hukumar yawon shakatawa ta Sin za ta ci gaba da goyon bayan bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa na HongKong

cri

A ran 15 ga wata, shugaban hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin Shao Qiwei ya yi bayani a shiyyar HongKong ta Sin, cewa hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin da kuma hukumomin da ke tafiyar da sana'ar yawon shakatawa ta duk fadin kasar za su ci gaba da goyon bayan bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa na HongKong kamar yadda su kan yi kullum, kuma za su inganta hadin gwiwa tare da sana'ar yawon shakatawa ta HongKong a fannonin tsara manufofi da raya kasuwa da bunkasa albarkatun kwadago.

Mr. Shao ya yi wannan bayani ne a gun liyafar da sassan yawon shakatawa na babban yankin kasar Sin da HongKong suka yi a ran nan domin murnar ranar cikon shekaru 10 da dawowar Hongkong cikin mahaifa ta kasar Sin.

Ban da wannan kuma a gun liyafar, Mr. Shao ya bayyana cewa, a cikin dogon lokaci, sassan yawon shakatawa na babban yankin kasar Sin da HongKong sun nuna goyon baya ga juna, da hadin gwiwarsu sosai, da kuma samun bunkasuwa gaba daya. Tare da kara yin cudanya tsakanin babban yankin Sin da HongKong wajen tattalin arziki da cinikayya a cikin shekaru 10 da suka gabata, bangarorin biyu su ma suna ta inganta hadin gwiwa da mu'amala tsakaninsu a fannin yawon shakatawa.(Kande Gao)