Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-15 18:46:29    
Lambun shan iska na Olympic cikin kurmi

cri

Aminai 'yan Afrika, lallai kun amince da cewa, kyakkyawan hasashe ne aka yi idan an hada Olympic da kyakkyawar shimfidar kurmi; kuma mutane za su ji dadi ainun idan sun samu damar kallon wasu gagaruman gasanni a cikin kurmi mai kayatarwa. To, a shekara mai zuwa, za a gudanar da gasannin wasan harba kibiya, da wasan kwallon tenis da kuma na wasan hoki a fili na wasannin Olympic na Beijing a cikin irin wannan kurmi mai launin kore-shar dake cikin birnin.

Jama'a masu saurare, abin da muke so mu gaya muku, shi ne rabin awa kawai ake bukata idan kun dauki mota zuwa arewacin birnin daga kwarkwaron zare na kewayayyar hanyar mota ta biyu ta arewacin birnin Beijing, inda za ku shiga wannan lambun shan iska na Olympic cikin kurmi.

An soma gina wannan lambun shan iska ne a ran 30 ga watan Yuni na shekarar 2005. Jimlar fadinsa ta kai kadada 680. Filin wasan kwallon hoki da filin wasa na harba kibiya da kuma filin wasan kwallon tenis na taron wasannin Olympic na Beijing suna a kudancin lambun shan iskar.

Fadin filin wasan kwallon hoki ya kai kimanin kadada 11.87, wanda ya rabu gida biyu, wadanda suke da kujeru 19,000; Fadin filin wasan harba kibiya ma ya kai kadada 9.22 ,wanda ke da kujeru 5,000; Ban da wannan kuma, cibiyar wasan kwallon tenis na da filaye 10 na yin gasa a kuma filaye 6 na horaswa, wadanda ke da kujeru 17,400. Filin wasan kwallon hoki da filin wasan harba kibiya na lambun shan iska na Olympic, dukansu filaye ne na wucin gadi, wato ke nan za a mai da su don su zama wucin ciyawa na lambun shan iska na Olympic bayan taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Sai dai filin wasan kwallon tenis ne kawai zai zama wani filin gasa na din-din-din.

Babban jigon shirin kasafin lambun shan iska cikin kurmi, shi ne " Kwarkwaron zare na zuwa halitta", wato ke nan a hada shimfidar birni kirar dan adam da kyakkyawan muhallin halitta na duwatsu da koguna gu daya. Hakan zai gwada wani " Kurmin halittu masu rai" wanda aka samo asalinsa daga halitta a gaban mazauna birnin Beijing.

Kewayayyar hanyar mota ta 5 ta Beijing ta raba lambun shan iska cikin sassa biyu wato sashen kudu da na arewa. Kuma abin da ya hada wadannan sassa biyu shi ne " Zauren kore-shar" dake ketare kewayyar hanyar mota ta 5, wanda kuma kuma yake kan kwarkwaron zare na birnin Beijing. Masu kasafin lambun shan iska suna kiran zauren a kan cewa "zauren halittu", wanda kuma yake kama da wata gada kan titi, inda kuma aka dasa tsire-tsire iri daban-daban. Ga wasu kananan dabbobi na kai da kawo yadda suka ga dama a sashen kudu da na arewa na lambun shan iska ta wannan gada. To, me ya sa aka gina irin wannan "zauren halittu"? Dalili kuwa shi ne saboda kewayayyar mota ta raba lambun shan iska sassa biyu. Idan idan ba a gina irin wannan gada, to lallai za a lalata tsarin halittu na wadannan sassa biyu. Saboda haka ne, masu kasafin suka yi amfani da wannan "zauren halittu" don hada tsarin halittu na sashen kudu da na arewa na lambun shan iska gu daya, ta yadda za a bada tabbaci ga samun ingantattun halittu na birnin Beijing. Kazalika, irin wannan kasafin da aka yi ya tsawaita kwarkwaron zare na kewayayyar hanyar mota ta 5 zuwa can nesa.

Ban da wannan " zauren halittu", domin rage tasiri da mutanen sukan yi ga muhallin halitta na lambun shan iska bisa harkokin da suke yi, masu kasafin suka tanadi cewa ya kamata a kiyaye sararin samaniya na dare idan an bude fitilu domin kare harkokin wasu dabbobi masu tafiya a dare da kuma barin jama'a su samu damar daba taurarin sararin samaniya.

Yanzu, an rigaya an kammala akasarin ayyukan dashen bishiyoyi da ciyayi a sashen arewa na lambun shan iska na Olympic cikin kurmi ,wanda fadinsa ya kai kadada 680; Ban da wannan kuma, an riga an kammala kashi 80 cikin kashi 100 na irin wadannan ayyuka a sashen kudu na lambun shan iskar. Amma duk da haka, ana bukatar samun wani dogon lokaci wajen kafa wani cikakken tsarin halittu na wannan lambun shan iska da aka gina da karfin lebura; kuma babu tantama, ba za a iya samun amfanin halittu na lambun shan iska tun da wuri ba, sai dai bayan taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Mutane na sa ran wannan lambun shan iska na Olympic zai kyautata yanayin sama na birnin Beijing sannu a hankali da kuma rage dumamar yanayi na birnin. ( Sani Wang )