Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-15 18:45:53    
Bangarori biyu na yankin tekun Taiwan sun tattauna sosai kan zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a tsakaninsu kai tsaye

cri

A karshen watan Afrilu da ya wuce, a nan birnin Beijing, hukumomi da abin ya shafa na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da Jam'iyyar Kuomintang ta Sin sun hada kansu sun shirya taron dandalin tattaunawa kan tattallin arziki da ciniki da al'adu a tsakanin bangarori biyu na yankin tekun Taiwan a karo na uku. Sa kaimi ga yin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a tsakanin bangarorin biyu kai tsaye, yana daya daga cikin shawarwari bai daya da aka samu a gun taron dangane da sa kaimi ga inganta ma'amala da hadin guiwa a tsakanin bangarorin biyu. Mahalartan taron suna ganin cewa, ya zuwa yanzu, ba a iya yin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a tsakanin bangarorin biyu kai tsaye, wannan ya zama wani tarnaki ne ga bunkasuwar tattalin arzikin Taiwan da ma'amala da hadin guiwa da ake yi a tsakaninsu a fannin tattalin arziki da ciniki.

Jimlar kudi da aka samu daga wajen ciniki a tsakanin babban yankin kasar Sin da Taiwan ta wuce dalar Amurka biliyan 100 a shekarar bara. Jama'ar Taiwan da suke kai da komowa a babban yankin kasar Sin su ma sun kai miliyan 4.4 a duk shekarar bara. Sabo da haka yin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a tsakanin bangarorin biyu kai tsaye babban bukatu ne da ake yi. Amma da yake cikas da hukumar Taiwan ke kawowa, yawancin mutane da kayayyaki na bangarorin biyu su kan yada zango a wani wuri daban, kafin su isa Taiwan ko babban yankin kasar Sin.

Shehun malama Dai Zuomin ta Jami'a mai suna "Chenggong" ta Taiwan tana ganin cewa, yanzu, babban yankin kasar Sin ya riga ya bude wa Taiwan kofar yin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a tsakaninsu kai tsaye. Ta ce, "a sakamakon zirga-zirgar jiragen sama da ruwa da ake yi a tsakanin bangarori biyu na yankin teku na Taiwan kai tsaye, yawan kudi da ake kashewa don yin zirga-zirgar zai ragu, sa'an nan yawan kudin riba da kamfanonin zirgar-zirgar jiragen ke samu zai karu."

Malam Yan Changshou, shugaban Hotel mai suna "Yadulizhi" ta Taiwan yana ganin cewa, idan an tabbatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a tsakanin bangarori biyu na yankin teku na Taiwan kai tsaye, to, za a mayar da Taiwan don ya zama wurin yada zango ga yin harkokin kasuwanci da yawon shakatawa, ta haka Taiwan zai sami babbar damar yin kasuwanci. Ya kara da cewa, "yayin da mutanen Taiwan da na babban yankin kasar Sin wadanda ke kai wa juna ziyara sun kara yawa, kuma yayin da za mu tsaya kan matsayi mai rinjaye na hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa, aiki da ya kamata mu yi shi ne, mu raya Taiwan da ya zama babbar cibiyar sufuri ga kudancin kasar Sin da kudu maso gabashin Asiya. Sa'an nan kuma Taiwan zai takara mai yakini a duk duniya, kuma zai kara samu damar kasuwanci da makoma mai kyau."

Mahalartan taron dandalin tattaunawa kan tattallin arziki da ciniki da al'adu a tsakanin bangarori biyu na yankin tekun Taiwan a karo na uku suna ganin cewa, idan an yi hange nesa, yin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa a tsakanin bangarorin biyu kai tsaye, zai ba da taimako ga zurfafa ma'amalar tattalin arziki da ciniki da hadin guiwa a tsakaninsu. A gun bikin rufe taron, Malam Zheng Lizhong, mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin Taiwan na Kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ya bayyana cewa, "mu sa kaimi ga kungiyoyin zirga-zirgar jiragen sama na jama'ar bangarorin biyu da su tattauna kan hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu kai tsaye tun da wuri. Kuma mu sa kaimi ga kungiyoyin sufuri na jama'ar bangarori biyu da su sami ra'ayi bai daya a kan al'amuran zirga-zirgar jiragen teku a trsakaninsu tun da wuri. Kamata ya yi, bangaren Taiwan ya amince da kamfanonin zirga-zirgar jiragen ruwa na babban yankin kasar da su kafa rassansu a Taiwan bisa manuforin taimakon juna da moriyar juna." (Halilu)