Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-14 19:08:02    
Kasar Sin za ta kara raya da kimiyya da fasahohin fama da sauyin yanayin duniya

cri

Yau, ran 14 ga wata, kasar Sin ta bayar da shirin "Matakan kimiyya da fasaha na musamman domin fama da sauyin yanayin duniya" domin daidaita ayyukan nazarin kimiyya da raya fasahohin fama da sauyin yanayin duniya da daga karfinta na fama da sauyin yanayin duniya. A wannan rana, Mr. Wan Gang, ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ba za ta nemi hanyar rage yawan abubuwa masu gurbata muhalli bayan da yawan irin wadannan abubuwa masu gurbata muhalli ya yi yawa sosai ba, amma za ta nemi hanyoyin kimiyya da fasahohin neman sulhu a tsakanin dan Adam da halittu iri iri lokacin da take neman bunkasuwa. A waje daya, Mr. Wan Gang yana fatan kasashe masu arziki za su iya nuna goyon baya ga masana'antunsu wajen mayar da sabbin fasahohin kiyaye muhalli da na makamashi ga kasashe masu tasowa domin neman wata hanyar neman cigaba ba tare da gurbata muhalli ba. A gun wani taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya, Mr. Wan Gang ya bayyana wa kafofin watsa labaru jerin burin da kasar Sin take son cimmawa wajen fama da sauyin yanayin duniya. Mr. Wan ya ce, "Ya zuwa shekarar 2020, karfin kirkirar sabbin fasahohin fama da sauyin yanayin duniya zai samu karfafuwa. Wasu muhimman fasahohin kayyade fitar da yawan hayakin da ke dumama yanayin duniya da sassauta saurin sauyin yanayin duniya da kasar Sin take da ikon mallakarsu za su samu cigaba, kuma za a yi amfani da wadannan fasaahohi daga duk fannoni. A waje daya, wasu muhimman masana'antu da yankuna za su karfafa karfinsu na dacewa da sauyin yanayin duniya."

Jama'a masu sauraro, kasar Sin za ta kara zuba kudade da horar da kwararru kan ayyukan nazarin kimiyya da raya fasahohin fama da sauyin yanayin duniya domin cimma wadannan buri. Kuma za ta kara yin hadin guiwa da kasashen waje a fannnin kimiyya da fasaha domin neman mayar da sabbin fasahohi a tsakanin kasa da kasa. Game da batun mayar da fasahohin fama da sauyin yanayin duniya a tsakanin kasa da kasa, Mr. Wan Gang ya nuna cewa, yana fatan kasashe masu arziki za su iya kara yin hadin guiwa da kasashe masu tasowa. Mr. Wan ya ce, "Muna fatan kasashe masu arziki za su iya nuna goyon baya ga masana'antunsu wajen mayar da sabbin fasahohin fama da sauyin yanayin duniya da na yin amfani da makamashin halittu ga kasashe masu tasowa. Kasashe masu tasowa za su iya mallaka da yin amfani da fasahohin da kasashe masu arziki suke sayar musu. Sabo da haka, za a samu wata hanyar neman cigaba amma ba tare da gurbata muhalli ba."

An bayyana cewa, masana'antu masu dimbin yawa sun riga sun shiga wannan aikin tsimin makamashin halittu da rage yawan abubuwan da ke dumama duniya da gurbata muhalli. Wasu masana'antun da suke amfani da makamashin halittu sosai sun soma yin amfani da abubuwan da suke fitarwa domin raya tattalin arzikin bola jari. Bugu da kari kuma, masana'antun kira na kasar Sin, musamman masana'antun kera motoci suna kuma kokarin kirkirar sabbin fasahohin tsimin makamashin halittu da kiyaye muhalli.

Mr. Wan Gang ya bayyana cewa, yanzu dukkan manyan masana'antun kera motoci na kasar Sin sun riga sun tsara shirin kera motoci masu tsimin makamashin halittu kuma masu yin amfani da sabbin makamashin halittu bisa manyan tsare-tsare. Kasar Sin ta riga ta soma yin amfani da motoci masu aiki da wutar lantarki ko masu aiki da karfin gaurayen makamashin gargajiya da na zamani a fannin babban zirga-zirga na jama'a a wasu manya da matsakaitan birane. Kasar Sin tana kan gaban duniya wajen yin amfani da motocin da suke amfani da gas maras gurbata muhalli. Mr. Wan Gang ya ce, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakan kimiyya da fasaha da manufofin haraji domin sa kaimi wajen raya sana'ar kera motoci masu kiyaye muhalli. Mr. Wan ya ce, "Fasahohin zamani na tsimin makamashin halittu da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli bukatu ne da ake nema domin neman bunkasuwar zaman al'ummarmu. Za a samu moriya a nan gaba bayan kaddamar da irin wadannan fasahohin zamani. Ina fatan masana'antu namu za su kara yin hadin guiwa da takwarorinsu na kasashen waje kan yin nazari da yin amfani da irin wadannan fasahohin zamani." (Sanusi Chen)