Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-13 17:41:54    
Kiyaye muhalli a kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Ibrahim Zubairu Othman, mai sauraronmu da ke birnin Zaria na jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wata wasikar da ya turo mana a kwanan baya, ya tambaye mu, shin wadanne irin hanyoyi ne hukumar kasar Sin take bi domin rage dumamar sararin sama, sabo da irin gurbatattun sinadaran da masana'antun suke fitarwa? Domin amsa tambayar, a cikin shirinmu na yau kuma, bari mu gutsura muku irin matakan da Sin ke dauka ta fuskar tinkarar matsalar sauye-sauyen yanayi.

A yayin da kankara ke narkewa a nahiyar Antartic, dazuzzuka a Afirka ma suna raguwa sannu a hankali. Dabbobin Bear da ke Turai ba su shiga barci ba a lokacin hunturu da ya wuce, kuma tsuntsayen da ke yada zango a tsakanin wurare daban daban bisa sauye-sauyen yanayi ma yanzu sun rasa inda za su tafi. Wani binciken da MDD ta yi ya yi nuni da cewa, koguna 250 na duniya suna busawa da saurin gaske?Matsalar muhalli tana ba mu mamaki, kuma tana ta jawo hankulan jama'a, har ma ta zamanto babbar barazana da ke gaban makomar dan Adam.

To, amma wa ya kawo matsalar? Amsa ita ce har kullum dan Adam suna rayuwa suna ci gaba ne tare da gurbata muhalli. Musamman ma tun daga karshen rabin karnin da ya wuce, a yayin da dukiyoyin da dan Adam ke tarawa suke ta karuwa, sabanin da ke tsakanin dan Adam da kuma muhalli ma ya tsananta.

A nan kasar Sin, a cikin shekaru kusan 30 da suka wuce tun bayan da Sin ta bude kofarta ga duniya da kuma yin gyare-gyare a gida, Sin ta cimma manyan nasarori a fannin ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma, amma a sa'i daya, matsalar gurbacewar muhalli ma ta taso har ma tana yi wa cigaban tattalin arziki tanarki da kuma kawo barazana kan zaman rayuwar jama'a. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai a kan kiyaye muhalli, kuma tana kokarin daukar matakai don bayar da nata taimako a wajen kiyaye muhallinta da na duniya baki daya.

A bayane ne gwamnatin kasar Sin ta gabatar da "raya zaman al'umma mai tsimin albarkatun kasa da kuma kiyaye muhalli" a matsayin wani burin da za a yi kokarin neman cimmawa. Musamman ma a cikin shirin ci gaban kasar Sin na 11 cikin shekaru biyar, wato daga shekarar 2005 zuwa 2010, gwamnatin kasar Sin ta tsara cewa, ya zuwa shekarar 2010, za a rage makamashin da ake yin amfani da su cikin kason GDP da kimanin kashi 20%, a yayin da za a rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli da kashi 10%.

Bayan haka, kwanan baya, wato a ranar 4 ga wata, Sin ta kuma bayar da shirin kasa kan tinkarar sauye-sauyen yanayi, wanda ya kasance takardar manufofi ta farko da Sin ta tsara don tinkarar sauye-sauyen yanayi daga dukan fannoni, haka kuma shirin kasa na farko ne da wata kasa mai tasowa ta tsara don fuskantar matsalar. Shirin ta yi nuni da cewa, Sin za ta dukufa a kan saukaka fitar da hayakin da zai iya haddasa dumamar yanayi, a sa'in da za ta kyautata karfinta na tinkarar sauye-sauyen yanayi.

Ban da wannan, don sassauta illolin da ayyukan dan adam ke kawo wa yanayi, Sin ta kuma dauki wasu matakai, ciki har da yin watsi da masana'antun da ke bukatar makamashi masu yawa da gaggauta bunkasa na'urorin yaki da gurbacewar muhalli da kuma kara tafiyar da dokoki ta fuskar kiyaye muhalli da kara fadakar da jama'a kan kiyaye muhalli. Daga shekarar 1980 har zuwa ta 2005, Sin ta yi ta dasa bishiyoyi, wadanda suka dauki hayakin carbon dioxide da yawansu ya kai ton biliyan 4.6 gaba daya.

Ranar 5 ga watan nan da muke ciki ranar muhalli ce ta duniya. Babban jigon ranar a wannan shekara shi ne "narkewar kankara, matsala ce mai tsanani.". Don mayar da martani a kan ranar, Sin ita ma ta gudanar da bukukuwa iri iri bisa jigon "rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli da kuma raya zaman al'umma mai kiyaye muhalli", wanda kuma ya bayyana niyyar kasar Sin a wajen rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli da kuma raya zaman al'umma mai kiyaye muhalli. A matsayinta na wata babbar kasa da ke daukar alhakin da ke bisa wuyanta, Sin tana bayar da nata taimako a wajen kiyaye muhallinta da na duniya baki daya, kuma za ta kara ba da taimakon a nan gaba.(Lubabatu)