
A ran 12 ga wata a Hongkong, wakilin musamman na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin a yankin musamman na Hongkong na kasar Sin Mr Lv Xinhua ya bayyana cewa, aikin kiyaye albarka da zaman karko a Hongkong ba kawai ya dace da babbar moriyar kasar Sin da ta Hongkong ba, har ma ya dace da moriyar masu zuba jari na kasa da kasa musamman masu zuba jari a Hongkong.
Mr Lv ya yi wannan bayani ne a gun taron liyafa na kungiyar manema labaru na kasashen waje da aka shirya. Mr Lv ya ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata tun da dawowar Hongkong a kasar Sin har zuwa yanzu, ana kiyaye albarka a Hongkong, ana kara kyautata zaman rayuwar jama'ar Hongkong, haka kuma ana kara samun wata al'umma mai jituwa a Hongkong. Hongkong da babban yankin kasar Sin suna kara hadin kansu a fannoni daban daban, haka kuma Hongkong yana rike da kyakkyawar dangantakar tattalin arziki da cinikayya da kasashen duniya.(Danladi)
|