Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-13 07:44:57    
Wasan kwallon billiards ya sami karbuwa sosai a kasar Sin

cri

Masu sauraro,kamar yadda kuka sani,`dan wasa daga kasar Sin Ding Junhui ya sami cikakkiyar nasara a gun dandalin wasan kwallon billiards iri na `Snooker` na duniya,ana kiransa da sunan `yaro mai ban mamaki`,ban da wannan kuma,`yar wasa daga kasar Sin Pan Xiaoting ita ma ta samu sakamako mai faranta ran mutane a gun gasannin kwallon billiards na matsayin duniya sau tarin yawa,ana kiranta da sunan `sarauniyar kwallo tara`,a sanadiyar haka,a kwana a tashi,wasan kwallon billiards ya sami karbuwa sosai a kasar Sin.Kwanakin baya ba da dadewa ba,aka fara gasar kwallon billiards ta mutane dubu goma na unguwoyin birnin Beijing na shekarar 2007 a birnin Beijing.Mutane kusan dubu ashirin wadanda ke nuna sha`awa kan wasan kwallon billiards sun shiga wannan gasa.An kimmanta cewa,yanzu yawan mutanen dake yin wasan kwallon billiards a kasar Sin ya riga ya kai wajen miliyan 60.Ana iya cewa,wasan kwallon billiards ya riga ya sami karbuwa daga duk fannoni a kasar Sin.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Wasan kwallon billiards ya shiga kasar Sin a shekarun 1980,amma a wancen lokaci,yawancin mutane wadanda suke yin wasan su ne samari wadanda suka rasa aikin yi,amma a sauran kasashe,ana kiran wasan da sunan `wasan masu ladabi`.Kawo yanzu,halin nan ya canja,masu yin wasan su ne masu ladabi.Ina dalilin da ya sa haka?

To,bari mu gaya maka cewa dalilin da ya sa haka shi ne domin amfanin abin koyi.Kafin shekarun da suka wuce,`dan wasa daga kasar Sin Yao Ming ya shiga kungiyar NBA,wannan ya sa yawan sinawa wadanda suke yin wasan kwallon kwando ya karu cikin sauri,daga baya kuma Li Ting da Sun Tiantian sun samu zakarun wasan kwallon tennis na taron wasannin Olimpic,wannan ya sa sinawa da yawan gaske suka fara yin wasan tennis.Yanzu dai,Ting Junhui da Pan Xiaoting su ma haka ne,a shekarar da ta wuce,Ding Junhui ya lashe `yan wasa tara wadanda suka fi yin suna a duniya ya samu zakaran gasar cin kofin kasar Ingila na `Snooker`,wannan ya sa sinawa suka fara nuna sha`awa kan wasan kwallon billiards.Mr.Jin wanda ya shiga gasar kwallon billiards ta mutane dubu goma na unguwoyin birnin Beijing ya gaya mana cewa,dalilin da ya sa ya fara yin wasan shi ne domin Ding Junhui.Ya ce:  `A da,ban taba yin wasan kwallon billiards ba,daga baya kuma na san Ding Junhui,na ji mamaki sosai saboda fasaharsa,yanzu na ji dadin wasan sosai.`

Ana iya cewa,wasan kwallon billiards ya riga ya samu karbuwa sosai a kasar Sin,amma ko ana iya cewa,halin da `yan wasan sana`a na wasan kwallon billiards na kasar Sin ke ciki ya sami kyautatuwa?Mr.Chen wanda ya samar da dakin gasa ga gasar kwallon billiards ta mutane dubu goma na unguwoyin birnin Beijing ya gaya mana cewa ba haka ba ne.Ya ce,kodayake yanzu yawan mutanen da suke yin wasan kwallon billiards ya karu bisa babban mataki,amma halin da `yan wasan sana`a na wasan ke ciki bai sami kyautatuwa a bayyane ba.Mr.Chen ya ce:  `Yanzu `yan wasan kwallon billiards wadanda su kan shiga gasa suna iya samun kudin Renminbi dubu 40 ko 50 a kowace shekara,wadannan `yan wasa su kan koyar da wasan su sami kudi daga baya kuma su shiga gasa da kudin da suka samu.Ban da wannan kuma,yanzu a kasar Sin,kudin da ake bai wa masu samun lambobin yabo ba yawa,wato kadan ne,alal misali,idan wani `dan wasa ya samu zakara,to,za a ba shi kudin Renminbi wajen dubu goma kawai.`

Mr.Chen ya fayyace cewa,`yan wasan sana`a su kan biyan kudin sufuri da na abinci da na dakin kwana da kansu,shi ya sa ba za su samu kudi daga gasa ba.Idan ana so a samu sakamakon da Ding Junhui da Pan Xiaoting suka samu,akwai wuya sosai,ya ce,  `A halin da ake ciki yanzu,wasan kwallon billiards ba wasa na taron wasannin Olimpic ba,gwamnatin kasar Sin ba ta kashe kudi da yawa kansa ba,dole ne `yan wasa su yi kokari da kansu,kuma kawo yanzu ba a kafa kungiyar wasan kwallon billiards ta kasa ba,shi ya sa bai kamata ba iyalai su koyi iyalan Ding Junhui da Pan Xiaoting su sa kaimi ga yaransu da su zama `yan wasan kwallon billiards na sana`a.`

Kodayake wasan kwallon billiards ya riga ya samu karbuwa sosai a kasar Sin,amma wasan kwallon billiards na sana`a a kasar Sin bai samu ci gaba ba,kuma ba a gudanar da kasuwar wasan yadda ya kamata ba,shi ya sa dole ne a ci gaba da sanya kokari kan wadannan fannoni.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)