Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-13 07:42:54    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (06/06-12/06)

cri

Ran 10 ga wata,an yi zagaye na karshe na gasar shahararrun kungiyoyin `yan wasan kwallon boli na mata a kasar Switzerland,kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Cuba da 3 bisa 0 ta zama zakara,kungiyar kasar Cuba ta samu lambatu,ban da wannan kuma,kungiyar kasar Holand ta samu lambatiri a bayansu.Gasar dake tsakanin shahararrun kungiyoyin `yan wasan kwallon boli na mata ta Switzerland ta yi suna sosai a duniya,ana saba yinsa sau daya a kowace shekara.A wannan shekara,gaba daya kungiyoyi takwas suka shiga gasar.

Ran 10 ga wata,`dan wasa daga kasar Sin Liu Xiang ya samu zakaran gasar gudun tsallake shinge na mita 110 ta maza da dakika 13 da 23 a gun babbar gasa ta ba da kyauta ta wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya da aka shirya a birnin Eugene na kasar Amurka.

Ran 10 ga wata,aka kammala gasar tsinduma cikin ruwa ta duniya ta Madrid ta shekarar 2007 a birnin Madrid na kasar Spain,a gun gasannin da aka yi,kungiyar kasar Sin ta samu cikakkiyar nasara,wato ta samu lambobin zinariya bakwai daga cikin adadin lambobi takwas na zinariya,`yan wasa 186 daga kasashe da shiyyoyi 23 suka shiga gasanni 8 da aka shirya.

Ran 9 ga wata,aka kammala gasar da aka shirya bisa gayyata ta wasan kwallon kafa ta samari ta duniya ta shekarar 2007 wato `Toulun Cup`.A gun zagaye na karshe na gasar,kungiyar Olimpic ta kasar Sin ba ta lashe kungiyar samari ta kasar Faransa ba wato ta samu lambatu kawai,daga nan kungiyar samari ta kasar Faransa ta zama zakara.Duk da haka,wannan shi ne sakamako mafi kyau da kungiyar `yan wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta samu a gun wannan shahararriyar gasar wasan kwallon kafa ta samari ta duniya ta gargajiya.A gun gasar nan,bi da bi ne kungiyar Olimpic ta kasar Sin ta lashe wasu kungiyoyi masu karfi kamarsu kungiyar samari ta kasar Holand da ta kasar Ghana da ta kasar Cote Divor da dai sauransu.(Jamila Zhou)