Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-12 17:26:52    
Yaran da ke samun kiba fiye da kima sun fi saukin kamuwa da cututtukan kafa

cri

Barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, yaran da ke samun kiba fiye da kima sun fi saukin kamuwa da cututtukan kafa, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan wani likitan da ke aiki a kauyukan kasar Sin wanda ake kiransa Ma Yupeng. To, yanzu ga bayanin.

Bayan da masu aikin likitanci na kasar Amurka suka gudanar da wani bincike cikin dogon lokaci, sun gano cewa, yaran da ke samun kiba fiye da kima sun fi saukin kamuwa da cututtukan kafa idan an kwatanta su da yaran da ke da nauyin jiki kamar yadda ya kamata.

Kwararren kasar Amurka a fannin aikin likitanci Daryl Hickok da abokan aikinsa sun bayar da wani rahoto, inda suka nuna cewa, idan yara sun samu kiba fiye da kima, to kafafunsu da suke girma za su dauki nauyi da kuma matsi fiye da kima, wanda zai iya lalata kafafunsu sosai.

Haka kuma Mr. Hickok ya bayyana cewa, kullum kafafun yara mata su kan girma kamar yadda ya kamata lokacin da shekarunsu ya kai 14 zuwa 15 da haihuwa, amma kullum kafafun yara maza su kan girma kamar yadda ya kamata lokacin da shekarunsu ya kai 15 zuwa 17 da haihuwa. Kafin wannan, kasusuwan kafafun yara sun fi saukin lalata sakamakon samun kiba fiye da kima, ta haka wadannan yara sun fi saukin kamuwa da cutar doron kafa da dai sauran cututtukan kafa.

Ban da wannan kuma wannan kwararre ya nuna cewa, a da yaran da ke son wasannin motsa jiki sosai su kan kamu da wadannan cututtukan da muka ambata a baya, amma yanzu yaran da ke samun kiba fiye da kima masu yawa suna kamuwa da cututtukan. Bayan da yaran da ke da kiba fiye da kima sun kamu da cututtukan kafa, su kan rage lokutan motsa jiki sakamakon jin zafin kafafunsu, wanda zai iya haddasa ci gaban karuwar nauyin jikinsu, ta haka wannan zai zama wani mumunan abu da ke faruwa.

Mr. Hickok yana ganin cewa, yaran da ke kamuwa da cututtukan kafa suna iya sa takalman musamman wajen gyara kafafunsu, kuma idan halin da suke ciki ya tsananata, to ana iya yin wa kafafunsu tiyata.

Ban da wannan kuma, bayan da masu ilmin kimiyya na kasar Faransa suka yi bincike, sun gano cewa, ba kawai samun kiba fiye da kima zai kara hadarin kamuwa da cutar hauhawar jini da dai sauran cututtuka ba, har ma zai iya rage basirar mutane.

Bisa labarin da wata jaridar kasar Birtaniya ta bayar, an ce, masu ilmin kimiyya na kasar Faransa sun gudanar da wata jarrabawar basira har ta tsawon shekaru biyar ga baligai fiye da 2200 da shekarunsu ya kai 32 zuwa 62 da haihuwa. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, a cikin kalmomin da ake cikin jarrabawar, mutanen da ke da jiki sosai suna iya tuna da kalmomin da yawansu ya kai 56 bisa dari, amma mutanen da ke samun kiba fiye da kima suna iya tuna da kalmomin da yawansu ya kai 44 bisa dari kawai.