Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-11 18:51:24    
Birnin Baoding na kasar Sin yana raya makamashin zafin rana

cri

A yawancin biranen kasar Sin, a kan yin amfani da wutar lantarki ga fitilun da ke ba da hannu ga ababen hawa. Amma a birnin Baoding na lardin Hebei da ke arewacin kasar Sin, wakilinmu ya gano cewa, akwai bambancin da ke tsakanin fitilun ba da hannu ga ababen hawa na birnin da na sauran wurare, wato akwai wani batir mai amfani da hasken rana a kan ko wace fitila, wanda ke iya sarrafa hasken rana zuwa makamashin wutar lantarki, ta haka fitilun da ke ba da hannu ga ababen hawa suna iya aiki kamar yadda ya kamata.

Game da irin wannan fitilar ba da hannu ga ababen hawa ta sabon salo, ba kawai makamashin da take yin amfani da shi ba zai kare ba, har ma yana da tsabta sosai. An labarta cewa, bayan da aka kaddamar da yin amfani da wadannan fitilu irin na sabon salo, nan da nan sun jawo hankulan mazaunan birnin Baoding. Kuma sun gaya mana cewa, " A ganina, irin wannan fitila tana da matukar kyau, ba kawai tana iya yin tsimin makamashi ba, har ma tana iya kiyaye muhalli. Ta haka za a kawo wa kasar Sin da kuma jama'ar Sin alheri sosai."

Liu Tao, wani jami'i na hukumar kula da zirga-zirga ta birnin Baoding ya gaya wa wakilinmu cewa, yanzu an riga an ajiye fitilun yin amfani da makamashin zafin rana wajen ba da hannu ga ababen hawa a mararrabu 22 na tituna, wato ke nan ya kai kashi 20 bisa dari na dukkan mararrabun titunan birnin. Kuma ya kara da cewa, "fitila mai amfani da makamashin zafin rana wajen ba da hannu ga ababen hawa tana da halayen musamman biyu, daya shi ne ta canja hanyar samar da wutar lantarki ta da, kuma tana tsimin makamashi. Dayan shi ne fitilar tana samun wutar lantarki ba tare da waya ba, shi ya sa lokacin da muke ajiye irin wannan filita, ba a bukatar binne waya a cikin kasa ba, sabo da haka an rage nauyin ayyukan ajiye wadannan filitu. "

Ban da sanya fitilun yin amfani da makamashin zafin rana wajen ba da hannu ga ababen hawa a wasu muhimman mararrabun tituna, gwamnatin birnin Baoding ta sanya filitu masu yin amfani da makamashin zafin rana a gefunan tituna masu yawa. Babban injiniya na ofishin kula da fitilun kan titi na birnin Zhao Wanzeng ya bayyana cewa, an fara sanya irin wadannan filitun kan titi a jere a shekarar da ta gabata, kuma ya zuwa yanzu, an riga an kaddamar da fitilu kusan 200 masu yin amfani da makamashin zafin rana a kan tituna. Ban da wannan kuma ya kara da cewa, "Kullum a kan yin amfani da fitilun da karfin ko wancensu ya kai watt 250 a gefunan tituna, kuma matsakaicin lokacin da a kan yin amfani da wadannan fitilun kan titi shi ne 10 awoyi a ko wace rana. Sabo da haka ko wace fitila za ta yi amfani da wutar lantarki kusan kilowatt uku a ko wace rana. Yawan kudin da muka kashe wajen fitilun kan titi a shekarar da ta gabata ya kai fiye da yuan miliyan 15. Amma tare da yaduwar kayayyakin tsimin makamashi da kuma fitilu masu yin amfani da makamashin zafin rana, yawan kudaden da za a kashe wajen wutar lantarki zai samu raguwa sosai."

Bugu da kari kuma Mr. Zhao ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, hukumar da abin ya shafa ta birnin za ta ajiye fitilu 50 masu yin amfani da makamashin zafin rana a gefunan manyan tituna biyu domin ci gaba da raya fitilu masu yin amfani da makamashin zafin rana.

Yanzu an riga an gudanar da ayyukan raya makamashin zafin rana a birnin Baoding a wasu lokatai, kuma sun samu sakamako mai kyau. Idan fitilu masu yin amfani da makamashin zafin rana da ke kan tituna kuma wadanda ke ba da hannu ga ababen hawa sun tattara hasken rana a yini guda, to za su iya aiki har kwanaki shida ko bakwai. Cao Jidong, mataimakin shugaban kwamitin bunkasuwa da gyare-gyare na birnin Baodong ya gaya wa wakilinmu cewa, a shekaru da dama masu zuwa, birnin Baoding zai raya makamashin zafin rana a fannonin fitilu da samar da ruwan zafi da kuma dumama daki domin mayar da birnin Baoding a matsayin wani birnin da ke yin amfani da makamashin zafin rana daga dukkan fannoni. Haka kuma ya kara da cewa, "muna fatan bayan shekaru uku ko biyar, za a iya yin amfani da makamashin zafin rana wajen tsarin haske na duk birnin, ciki har da fitilun kan titi da na ba da hannu ga ababen hawa da na wuraren shan iska da dai sauransu. Kuma za mu yi amfani da makamashin zafin rana wajen dumama daki a cikin unguwannin da za a kafa. Haka kuma a wadannann unguwanni, dole ne a yin amfani da makamashin wajen wanka a lokacin zafi. Muna yin imanin cewa, bisa kokarin da muka yi a wadannan shekaru uku ko biyar, za mu cimma burinmu wajen mayar da birnin Baoding a matsayin wani birnin da ke yin amfani da makamashin zafin rana daga dukkan fannoni. " (Kande Gao)