Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-11 18:38:15    
Halartar taron tattaunawar 'G8+5' da shugaban Sin ya yi da kuma ziyarar da ya kai wa Sweden sun sami sakamako mai kyau

cri

Tun daga ran 6 zuwa ran 10 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya halarci taron tattaunawa a tsakanin shugabannin kasashe mambobin kungiyar G8 da kasashe 5 masu tasowa a kasar Jamus, bisa gayyatar da aka yi masa, ya kuma kai ziyarar aiki ga kasar Sweden. A ran 11 ga wata, ya dawo birnin Beijing. A kan hanyar dawowar kasar Sin, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi, wanda ya raka shugaban, ya yi wa manema labaru bayani kan sakamakon da aka samu daga wajen wannan ziyara. Yana ganin cewa, ziyarar da shugaba Hu ya yi ta habaka ra'ayi daya da aka samu, da kara fahimtar juna da kuma sa kaimi kan samun nasara tare. Ziyarar da shugaba Hu ya yi a wannan karo ta sami sakamako mai kyau kuma a bayyane.

A cikin kwanaki 4 kawai, shugaba Hu Jiantao ya halarci taruruka fiye da 30, ya kuma gana da shugabannin wasu kasashen duniya, inda ya bayyana ra'ayi da matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai a kan wasu al'amuran da ke jawo hankulan kasashen duniya.

Sauye-sauyen yanayin duniya muhimmin batu ne da shugabannin kasashe mambobin kungiyar G8 da kasashe 5 masu tasowa suka mai da hankulansu a kai a gun taron tattaunawar. A gun taron, shugaba Hu ya jaddada cewa, dalilin da ya haddasa sauye-sauyen yanayi shi ne neman bunkasuwa, ya kamata kasashen duniya su samar da sabon ra'ayi kan raba moriya da kuma sabuwar hanyar hada gwiwa, su kuma hada kansu kamar yadda ya kamata. Dole ne kasashen duniya su bi ka'idar daukar nauyi tare, amma bisa karfinsu a harkokin sauye-sauyen yanayi. Ya kamata kasashe masu sukuni su bai wa kasashe masu tasowa taimako, su kuma dauki jagoranci wajen daukar nauyin rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli bisa wuyansu. Ba a cancanci a gabatar da bukata ga kasashe masu tasowa a wannan fanni ba bisa son ransu ba a cikin halin yanzu. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin tana son ci gaba da hada kanta da kasashen duniya wajen daidaita sauye-sauyen yanayi da hada gwiwa da takwarorinta masu tasowa.

Mr. Yang ya bayyana cewa, ra'ayin da shugaba Hu ya bayyana ya nuna cewa, kasar Sin tana nuna ra'ayi mai yakini, tana kuma daukar nauyi bisa wuyanta kan al'amura da yawa. Akasarin ra'ayin jama'a na duniya ya yi hasashen cewa, jawabin Hu Jintao ya nuna wa kasashen duniya matsayin kasashe masu tasowa, wato suna neman daidaita sauye-sauyen yanayi tare cikin adalci.

A gun tattaunawa a tsakanin kasashe masu tasowa, shugaba Hu ya bayyana cewa, a cikin sabon halin da ake ciki, kamata ya yi kasashe masu tasowa su kara hada kansu, su daidaita kalubale ta fuskar dinkuwar tattalin arzikin duniya gu daya tare, su kiyaye moriyarsu ta bai daya. Ban da wannan kuma, ya kamata su dora muhimmanci kan sa kaimi wajen fito da kyawawan tsarin tattalin arzikin duniya da muhalli ta fuskar kudi da ciniki da makamakashi, ta haka za su iya kara samun iko wajen bayyana ra'ayoyinsu a harkokin tattalin arzikin duniya.

Mr. Yang ya kara da cewa, shawarar da shugaba Hu ya gabatar ta sami amincewa daga shugabannin da suka halarci taron da hannu biyu biyu.

A yayin da yake halartar taron tattaunawar, shugaba Hu ya gana da shugabannin kasashe 12 bi da bi, inda suka tattauna kan al'amuran da ke jawo hankulansu dukka, kamar su batun nukiliya na zirin Korea da kuma batun yankin Darfur na kasar Sudan. Dukkan shugabannin sun nuna babban yabo ga kasar Sin saboda kyakkyawar rawar da take takawa a harkokin shiyyar da take ciki da na duniya, sun bayyana cewa, za su kara hada gwiwa da Sin domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da kuma zabura wajen samun ci gaba tare.

Saboda haka ne, Yang Jiechi ya takaita ziyarar da shugaba Hu Jintao ya yi a wannan karo da cewa, halartar taron tattaunawa a tsakanin shugabannin kasashe mambobin kungiyar G8 da kasashe 5 masu tasowa da kuma ziyarar da ya kai wa kasar Sweden sun ci narasa a fannin hakaba ra'ayi daya da aka samu, da kara fahimtar juna da kuma sa kaimi kan samun narasa tare.(Tasallah)