Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-08 21:25:23    
Taron koli na G8 ya sami ra'ayi iri daya har ma ba kamar yadda ake tsammani ba

cri
Ran 7 ga wata, a birnin Heiligendamm na kasar Jamus, shugabannin rukunin kasashen G8 sun gana da juna, don tattaunawa kan batutuwa da yawa na kiyaye yanayi, da samar da makamashi yadda ya kamata, da ba da gudummuwa ga Afrika, da bunkasa tattalin arzikin duniya da sauransu. Amma abin da ya faru ba kamar yadda ake tsammani ba shi ne, rukunin kasashen G8 sun sami ra'ayi na bai daya kan manyan batutuwa da yawa da suka tattauna, wadanda kuma aka yi hasashen cewa za a sami gardama da baraka a kai kafin taron.

Na daya, a gun taron kolin, rukunin kasashen G8 sun sami babban ci gaba wajen kiyaye yanayi. Shugabannin kasashe daban daban sun sami ra'ayi iri daya a kan cewa, wajibi ne, a tsanake, a yi la'akari da tsaida manufofi da za a bi game da rage fitar da yawan hayaki mai daumamar yanayi, wato yawan hayakin da za a fitar a shekarar 2050 zai ragu da a kalla kashi 50 cikin dari bisa na shekarar 1990. Bayan taron, Madam Angela Merkel, firayim ministar kasar Jamus ta bayyana cewa, kasashen rukunin G8 gaba daya sun amince da cewa, a gun taron majalisar dinkin duniya kan harkokin muhalli da za a shirya a kasar Indonesiya a karshen shekarar nan, bangarori daban daban za su tattauna batun sauyewar yanayin duniya a karkashin inguwar majalisar dinkin duniya. Wannan karo ne na farko, kasashe 8 na rukunin G8 sun bayyana a fili cewa, sun amince da muhimmiyar rawa da majalisar dinkin duniya ke takawa wajen daidaita batun kiyaye yanayi.

Na biyu, cacar baki da kasashen Amurka da Rasha ke yi kan batun garkuwar kakkabo makamai masu linzami da Amurka ke kafawa a tsakiyar Turai ta sami sauyawa ba zato ba tsamamni a gun taron kolin nan. Kafin taron, kasashen biyu sun yi cacar baki mai zafi a kan wannan batu. Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha ya taba yin barazanar cewa, makamai masu linzami na kasarsa za su duba takitin Turai. A cikin irin wannan hali ne, a lokacin da Putin ke ganawa da Bush, shugaban kasar Amurka, ya gabatar da shawara da ke ba Bush da duk duniya mamaki, wato kasar Amurka za ta kafa garkuwar kakkabo makamai masu linzami a kasar Azerbaijan da ke makwabtaka da kasar Iran, don magance barzanar makamai masu linzami wadda mai yiwuwa ne kasar Iran za ta yi, ta haka bai kamata kasar Amurka ta kafa irin wannan garkuwar kakkabo makamai masu linzami a tsakiyar Turai ba. Sa'an nan makamai masu linzami na kasar Rasha ma ba za su duba takitin Turai ba. A zahiri, Bush ya yi mamaki da shawarar da Putin ya gabatar, har bai san amincewa ko kiyewa da ya nuna ba, sai ya ce, shawarar Putin aba ce mai ban sha'awa, hadin guiwa ya fi haddasa hali mai zafi kyau sosai. An ruwaito cewa, a lokacin da Putin zai kai ziyara a kasar Amurka a ran 1 ga watan gobe, za su ci gaba da tattaunawa a kan wannan batu.

Na uku, rukunin kasashen G8 sun nuna ra'ayi mai yakini kan halin da ake ciki yanzu dangane da harkokin tattalin arzikin duniya. Kafin taron, kwararru suna ganin cewa, ana zura ido kan batutuwa da za a daidaita game da rashin daidaituwar tattalin arziki da duniya ke fuskanta, da gibin kudin ciniki da kasashen Turai da Amurka ke samu, da rarar kudin ciniki da kasashe masu tasowa ke samu, da kuma karuwar darajar kudaden kasashen Asiya. Amma cikin sanarwar da shugabannin rukunin kasashen G8 suka bayar bayan taron, ana ganin cewa, harkokokin tattalin arzikin duniya suna gudana da kyau.

Ban da wadannan kuma, taron ya sami ra'ayi na bai daya kan inganta tattaunawa da za su yi tare da manyan kasashe masu tasowa. Kasar Jamus tana ganin cewa, ya kamata, rukunin kasashen G8 ya kara kokari wajen shigar da kasashen Sin da Indiya da Brazil da Mexico da Afrika ta kudu cikin tsarin gamayyar kasa da kasa, kuma su kafa tsarin tattaunawa tare da wadannan kasashe.

Lalle, taron koli na rukunin kasashen G8 bai sami ra'ayi iri daya a kan duk batutuwa ba. Alal misali, ya kasance da baraka a tsakanin kasashen Rasha da Amurka a kan mtsayin karshe na Kosovo, a kan batun Darfur, Bush ya yi gunaguni ga gamayyar kasa da kasa wadda ya zuwa yanzu ba ta dauki tsauraran matakai wajen daidaita batun, kuma cewar ya yi, mai yiwuwa ne, kasar Amurka za ta dauki matakin kashin kai.(Halilu)