Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-07 21:38:32    
Ma'daba'o'in kasar Sin sun kara hadin guiwar da ke tsakaninsu da kafofin watsa labaru da dama don sa kaimi ga wadatar da ayyukan madaba'a

cri

Kwanan baya, an yi taron baje kolin littattafai na karo na 17 na kasar Sin , wato kasuwar sayar da littattafai ta kasar Sin a birnin Chongqing da ke kudancin kasar Sin. Taron ya bayyana sabon halin da kasar Sin take ciki wajen aiwatar da harkokin madaba'a, wato masana'antun 'da'bi sun yi hadin guiwa da shirye-shiryen TV da na Rediyo don buga littattafai da kuma sayar da littattafai tare da tashoshin internet don sa kaimi ga raya madaba'o'i.

Daga shekarar 1980 ne kasar Sin ta soma shirya taron baje kolin littattafai na duk kasar, shi ya sa an mai da hankali sosai ga wannan taron baje koli, kuma an mayar da shi bisa dama mai muhimmanci da aka samu wajen yin cinikayyar littattafai da kaset-kaset da dai sauransu. Yawan wadanda suka halarci wannan taron baje koli ya kai sassa fiye da 1600, kuma yawan littattafai da kayayyakin kaset-kaset da irin na lantarki da na internet sun kai ire-ire dubu 260 ko fiye, an kimanta cea, yawan kudadden da rukunoni daban daban suka kashe domin sayi wadannan kayayyaki zai kai kudin Sin Yuan miliyan 50.

Shugaban babbar hukumar madaba'ar watsa labaru ta kasar Sin Mr Liu Binjie ya bayyana cewa, shirya taron baje kolin don nuna karfin kasar Sin wajen ayyukan dabi, ya ce, bisa albarkacin kara zurfafa gyare-gyaren da aka yi kan ayyukan dabi a kasar Sin, ana nan ana kara samun wadatuwa da bunkasuwa sosai wajen watsa labaru da aikin dabi, an buga wasu nagartattun littattafai da dai sauran kayayyakin al'adu da yawa, an kuma kafa wasu rukunonin madaba'o'I da ke da karfi sosai tare da ba da tasirinsu mai kyau da na jaridu da na sayar da kayayyakinsu. Hakikanin karfinsu da sakamakon da suka samu wajen yin kirkire-kirkire suna ta kara daguwa, kuma iyawarsu na samar da hidima ga jama'ar farar hula da matsayinsu sai kara daguwa suke yi.

A wurin taron baje kolin, an nuna sha'awa sosai wajen sayi littattafai dangane da wasu wasannin kwaikwayo da aka nuna a cikin shirye-shiryen TV, sa'anan kuma wasu littattafan da aka buga dangane da wani karin bayanan da wasu shehunan malamai na jami'ar Qinghua suka gabatar kan tarihin kasar Sin da wasu shahararrun littattafai na zamani aru aru na kasar Sin a cikin shirye-shiryen TV. Amma a da a tarihin kasar Sin , ba hakan aka yi ba.

Wata shehun malama Yu Dan ta yi amfani da tunanin zamani wajen ba da karin bayanai kan littattafan zamani aru-aru na kasar Sin ta hanyar shirye-shiryen TV, sa'anan kuma an buga littattafan da yawansu ya kai dubu 600 dangane da wadannan bayyanai, kuma an sayar da su dukka dukka da sauri, wasu masu ba da sharhi kan littafin sun bayyana cewa, Malama Yu Dan ta yi amfani da ra'ayoyin jama'ar farar hula wajen ba da karin bayanai a kan ilmi a cikin littafin, ta ba da gudumuwa ga yada al'adun kasar Sin.

Wata mataimakiyar direkta ta hukumar kula da harkokin buga littattafai ta kasar Sin malama Qi Yao ta bayyana cewa, a karshen watan Nuwanba na shekarar da ta gabata, mun soma sayar da littafin, ya zuwa yanzu, yawansu ya kai miliyan 3.8, a ganina, wannan ne mafi yawa a fannin, a farkon buga littafin, ba mu yi tsamanin adadin nan da muka samu ba.

Lokacin da ma'aikaciyar kamfanin dabi na lardin Liaoning na kasar Sin ta karbi ziyarar da wakilin gidan rediyo kasar Sin ya yi mata, ta bayyana cewa, irin hadin guiwar nan, kamfanonin dabi da yawa suke yi, kuma yawacinsu sun sami nasara.(Halima)