Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-07 15:59:38    
Jam'iyyun siyasa na demakuradiya da suke sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin

cri
 

Jam'iyyar demakuradiya ta shida dake sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce Jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin.Jam'iyyar ta hada da manyan da daidaiku na sinnawan da suka dawo daga ketare da kuma iyalansu da kuma mutanen dake da alaka da kasashen ketare.

A watan Oktoba na shekara ta 1925 a birnin Los Angeles na Amurka ne wata kungiyar Zhigong ta sinnawan dake zama a latin Amurka ta kafa wannan jam'iyya.Cikin dogon lokaci jam'iyyar Zhigong ta yi gwagwarmaya domin neman mulkin kai da 'yancin kasa da kuma kare moriyar adalci ta sinawan da ke zama a kasashen ketare.A taron wakilan kasa a karo na uku da aka yi a watan Mayu na shekara ta 1947,jam'iyyar Zhigong ta yi garambawul,daga nan ta kama hanyar ba da sahihin hadin kai ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da yin gwagwarnmaya tare.Cikin bin manyan ka'idojin da aka tanada a cikin tsarin mulkin kasa na Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin,jam'iyyar Zhigong ta kasar Sin tana tafiyar da harkokinta cikin yanci.Jam'iyyar Kwaminis ta Sin jam'iyya ce dake tafiyar da harkokin mulkin kasa,jam'iyyar Zhigong ta ba cikakken hadin kai,tana dukufa kain da nain wajen bunkasa zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin.

Jam'iyyar demakuradiya ta bakwai da ke sa hannunta cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce jam'iyyar nazarin ilimi ta ran 3 ga watan Nuwanba.manyan masana da madaidaiku masu ilimi ne a fannin nazarin ilimin kimiyya da fasaha su ne gishinkan jam'iyyar nan,jam'iyyar ta karbi shugabancin jam'iyyar kwaminis ta Sin ta hada kanta sosai da Jam'iyyar kwaminis ta Sin tana kokarin gina zaman gurguzu mai halayen musamman na kasar Sin.

Asalin jam'iyyar ya zo ne daga wata kungiyar tattaunawa ilimin kimiyya na demakuradiya da wasu masana masu kishin kasa dake yin dagiya da mayaudara imperism a turance suka kafa a birnin Chongqing tare da nufin neman demakuradiya da kimiyya.Domin tunawa da babbar nasara da aka samu a cikin yakin kin harin Japan da yakin kin 'yan fasist na duniya a ran 3 ga watan Satumba na shekara ta 1945 aka canja sunan jam'iyyar zuwa jam'iyyar nazarin ilimi ta ran 3 ga watan Satumba,a hukunce aka kafa jam'iyyar a ran 4 ga watan Mayu na shekara ta 1946.Jam'iyyar tana da nata kwamiti ko kwamitin share fage a larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da biranen dake karkashin jagorancin gwamnatin tsakiya su talatin da sauran birane da gundumomi 268 ban da Taiwan da Tibet.'ya'yan jam'iyyar sun kai dubu 88,kashi 60 bisa dari masana ilimi mai zurfi ne.

Jam'iyyar demakuradiya ta takwas dake sa hannu cikin harkokin siyasa na kasar Sin ita ce kawancen mulkin kai na demakuradiya na Taiwan.A ran 12 ga watan Nuwanba na shekara ta 1947 a birnin Hongkong ne aka kafa shi wanda ya hada ma'aikata da masu kishin kasa da suka zo daga lardin Taiwan,jam'iyyar siyasa ce dake bautawa gurguzu,kawancen ya ba da cikakken hadin kai ga Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.An kaurar da hedkwatar kwamitin tsakiya na kawancen nan daga Taiwan daga Taiwan zuwa babban yankin kasar Sin a shekara ta 1949,da farko an kafa hedkwatar a birnin Shanghai,an kaurar da ita zuwa birnin Beijing a shekara ta 1955.(Ali)


1 2 3