
Yau Alhamis, jarida ' China Daily' ta kasar Sin ta bayar da wani bayani na mai yin sharha, wanda ya fadi cewa, muhimmiyar doka ta yankin Hongkong, wani kyakkyawan shiri ne dake iya jurewa duddubawa daga yunkurin aikatawa.
Bayanin ya ce, yanzu ya kasance da zama mai dorewa da wadatuwar tattalin arziki da ci gaban demokuradiyya da kuma rayayyen karfi a yankin musamman na Hongkong. Hakikanan abubuwa da aka samu tun bayan da aka dawo da Hongkong cikin kasar mahaifa sun shaida ,cewa manufar ' Kasa daya amma tsarin mulki iri biyu' na dacewa da hakikanin halin da ake ciki a yankin, kuma yana dacewa da babbar moriyar kasa da jama'a.

Sa'anann bayanin ya jaddada, cewa muhimmiyar doka ta Hongkong wadda aka kaddamar da ita a shekarar 1990 da kuma soma gudanar da ita a shekarar 1997, wata takardar shari'a ce mai ma'anar tarihi da ta kasa da kasa.( Sani Wang )
|