Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-06 15:28:32    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(31/05-06/06)

cri
Da farko dai akwai wani labari game da taron wasannin Olympic na Beijing da za a yi a shekara mai zuwa, an ce, a ran 30 ga watan Mayu, a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, an bude babban taron kafa kwamitin kimiyya da kwamitin shirya babban taron kimiyyar wasan Olympic na shekara ta 2008. Shugaba Liu Peng na kwamitin wasan Olympic na kasar Sin da jami'an wasu kungiyoyin wasannin motsa jiki na kasa da kasa da kuma kwararru masu aikin kimiyyar wasannin motsa jiki na kasa da kasa sun halarci wannan babban taro. An saba shirya babban taron kimiyyar wasan Olympic a cikin kasar da za ta shirya taron wasanin Olympic kafin bude taron wasannin Olympic, a kan tattauna kan kimiyya da aikin ba da ilmi da kuma likitanci ta fuskar wasannin Olympic na duniya a gun taron, wannan babban taro muhmmin bangare ne na abubuwan tarihi na taron wasannin Olympic.

Ban da wannan kuma, a kwanan baya, ma'aikatan kwastam na yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin sun gudanar da aikin yaki da kayayyakin jabu, inda suka kwace kayayyaki jabu 350 da suka saci ikon mallakar ilmi na wasannin Olympic, wadanda darajarsu ta kai misalin kudin Hong Kong yuan dubu 7, an yi zane-zanen 'Fuwa' wato alamar nuna fatan alheri ta taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008 a kan yawancin kayayyakin. Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing shi ne ya ba da taimako wajen gudanar da wannan aikin yaki da kayayyakin jabu.

Ran 2 ga wannan wata, a gun gasar ba da babbar kyauta ta wasan tsalle-tsalle da guje-guje ta Reekok da aka yi a birnin New York na kasar Amurka, shahararren dan wasa Liu Xiang na kasar Sin ya zama zakara a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 da dakikoki 12 da wani abu, ya kuma sami maki mafi kyau a duk duniya a wannan shekara.

A gun babban taron hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa da kasa wato FIFA da aka yi a ran 31 ga watan Mayu, an tsai da kuduri cewa, shugaba mai ci S. Blatter ya sake hawan kan karagar mulkin kungiyar FIFA. Wannan ne karo na 2 da ya sake zama shugaban kungiyar FIFA. Zai shugabanci kungiyar FIFA zuwa shekara ta 2011 mai zuwa. (Tasallah)