Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-05 15:20:07    
Shayar da nono ga jarirai zai taimaka wa mata wajen rage hadarin kamu wa da cutar zuciya

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, Shayar da nono ga jarirai zai taimaka wa mata wajen rage hadarin kamuwa da cutar zuciya, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan nauyin karatu fiye da kima da ke bisa wuyan 'yan makarantu na kasar Sin. To, yanzu ga bayanin.

Ba kawai shayar da nono zai amfana wa jarirai sosai wajen lafiyar jiki ba, har ma zai kawo wa iyaye mata alheri sosai. Bisa wani nazarin da masu ilmin kimiyya na kasar Amuka suka yi a kwanan nan, an ce, shayar da nono ga jarirai zai taimaka wa mata wajen rage hadarin kamuwa da cutar zuciya.

Bisa labarin da mujallar 'Sabbin masu ilmin kimiyya' ta bayar, an ce, manazarta na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar Harvard ta kasar Amurka sun gudanar da wani bincike ga nas-nas 96648 da suka yi haihuwa daga shekara ta 1986 zuwa shekara ta 2002. Daga baya kuma sun gano cewa, hadarin kamuwa da cutar zuciya ga matan da suka shayar da nono ga jariransu har shekaru biyu ya yi kadan sosai idan an kwantanta su da matan da ba su taba shayar da nono ga jarirai ba.

Manazarta sun bayyana cewa, watakila shayar da nono ga jarirai zai ba da taimako ga mata wajen canja sauye-sauyen halitta daga salon irin na samun ciki zuwa salon kamar yadda ya kamata. Lokacin da mata suke da ciki, a kan fi samun kitse masu yawa a cikin jikinsu, haka kuma yawan sinadarin fatty acid da ke cikin jininsu ya yi yawa a gwargwado. Ta hanyar shayar da nono ga jarirai, mata za su iya canja wadannan kitsen da ke jikinsu zuwa abubuwan gina jiki da jarirai suka bukata.

Mr. Alison da ya kula da wannan binciken ya ba da shawarar cewa, ya fi kyau mata sun shayar da nono ga jarirai har watanni 3 zuwa shekara guda bayan da suka haihu.

Haka kuma bisa binciken da asusun yara na MDD ya gudanar ga kasashe masu tasowa, an ce, yawan jarirai masu shan nonon iyaye mata da suke da rayuwa ya ninka kusan sau biyu idan an kwantanta shi da jariran da ba su taba shan nonon iyaye mata ba. Haka kuma shayar da nonon iyaye mata kawai ga jarirai a cikin watanni shida bayan da aka haife su zai kawo musu alheri sosai wajen girmansu, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da nonon iyaye mata ya iya samar da muhimman abubuwan gina jiki da jarirai suke bukata, da kuma shawo kan wasu cututtuka masu tsanani.

Sabo da haka asusun yara na MDD yana ganin cewa, hanya mafi kyau wajen ciyar da jarirai ita ce shayar da nonon iyaye mata kawai gare su a cikin watanni shida bayan da aka haihe su, daga baya kuma an ci gaba da shayar da nonon iyaye mata ga jarirai bayan watanni 6, a waje daya kuma an kara sauran abinci yadda ya kamata har shekarunsu ya kai 2 da wani abu da haihuwa.(Kande)