Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-05 15:13:58    
Kogon dutse na Ludiyan da ke jihar Guangxi ta kasar Sin

cri

A cikin shirinmu na yau, kamar yadda muka saba yi, da farko dai za mu karanta muku wasu abubuwa kan kogon dutse na Ludiyan da ke jihar kabilar Zhuang ta Guangxi mai tafiyar da harkokinta da kanta, daga baya kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'Kallon jerin fitilu a Huangyuan na lardin Qinghai'.

Kogon dutsen Ludiyan shi ne kogon dutse mafi girma a birnin Guilin na jihar kabilar Zhuang ta Guangxi mai tafiyar da harkokinta da kanta, ya kuma fi nuna sigar musamman na yanayin kasa irin nan Karst. A cikin wannan kogon dutse, akwai duwatsu irin na stalactite da na stalagmite da yawa masu tsawo misalin mita 500. Ban da wannan kuma, kogon dutsen Ludiyan ya yi suna ne a matsayin wata fadar nuna fasahar halitta. In ya kasance da haske, to, duwatsu irin na limestone da ke cike da ma'adinai suna yin kama da murjani da jajaye da kuma fararen lu'ulu'u, a ganin masu yawon shakatawa, duwatsun suna kasancewa tamkar rumfuna da kyakkyawan babban zaure da lambunan da ke noman furanni da itatuwa masu ba da 'ya'ya.

Akwai wani babban farin dutse daga rufin kogon dutsen zuwa kasa, wanda ya yi kama da wata babbar magangarar ruwa. Wani dutsen da ya yi kama da wani tsohon shehun malami ya kasance a cikin wata barandar da ke babban zauren. Akwai wata almara game da ainihin asalin wannan dutse. A can da wani shehun malami ya je Guilin domin ganin ni'imtattun wurare, ya nuna sha'awa sosai kan kogon dutsen Ludiyan, ya tsai da kudurin rubuta wata waka. Amma ya dade bai iya kammala wannan waka ba, bai iya sifanta kyan ganin wannan kogon dutse ba, kafin ya kammala wakarsa, ya zama wani dutse. Wani babban dakin da ke cikin kogon dutsen ya iya daukar mutane dubu daya, an kira shi fadar lu'ulu'u ta sarkin Dragon bisa tatsuniyar gargajiya ta kasar Sin. An mayar da wani babban ginshikin dutse tamkar sandar dabo ta sarkin Dragon, wadda take iya kiyaye kwanciyar hankali a teku. A cikin shahararren kagaggen littafi mai suna 'Tatsuniyoyin wani biri mai wayo da ake kira Sun Wukong', sarkin birai wai shi Sun Wukong ya roki sarkin Dragon domin samun wannan sandar dabo, amma sarkin Dragon ya ki, shi ya sa sarkin birai ya kwace ta da karfi, ya samu galaba a kan sojojin sarkin Dragon, ya kuma tada hargitsi a cikin fadar sarkin Dragon domin mayar da martani. Duwatsun irin na stalagmite da ke cikin kogon dutsen sun yi kama da sojojin sarkin Dragon, kamar su dodon kodi da jellyfish.

Bayan da suka kai ziyara ga kogon dutsen Ludiyan, masu yawon shakatawa su kan yi tsammanin cewa, akwai kogunan dutse a cikin dukkan manyan tsaunuka, amma ba a iya san mene ne ke cikin kogunan dutsen ba.(Tasallah)