Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-01 18:53:31    
An soma odar tikitocin shiga na taron wasannin Olympic na Beijing ga duk duniya a hukumance

cri

A ran 15 ga watan Afrilu na shekarar da muke ciki, a nan birnin Beijing, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gudanar da wani "Taron watsa labarai kan yunkurin sayar da tikitocin shiga na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008", in da ya shelanta, cewa tun daga wannan rana ne aka soma yin odar tikitocin shiga na taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 ga fadin duk duniya a hukumance.

Mr. Wang Wei, babban sakatare kuma mataimakin shugaban zartarwa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi cikaken bayani kan yadda za a yi odar tikitocin shiga. Ya shelanta, cewa tun daga wannan rana, za a soma karbar odar tikiticon shiga na taron wasannin Olympic na Beijing da yawansu ya kai kimanin miliyan 7 daga jama'a; kuma kashi kimanin 75 daga cikinsu, za a sayar da su a cikin gidan kasar; sauran kashi kimanin 25 kuma za a sayar da su ne a ketare.

Sa'annan Mr. Wang Wei ya furta, cewa hanya mafi kyau da za a bi wajen sayen tikitocin shiga, ita ce tashar internet wadda cibiyar kula da harkokin tikitoci ta kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ta bude. Adireshin tashar internet shi ne: tickets. Beijing 2008. cn; Ban da wannan kuma, jama'a na yankin Hongkong da na Macao na kasar Sin na iya yin odar tikiti ta kwamitin wasannin Olympic na Hongkong da kuma hukumar bunkasa wasannin motsa jiki ta gwamnatin yankin musamman na Macao na kasar Sin. Jama'ar yankin Taiwan na kasar Sin na iya sayen tikiti ta kwamitin wasannin Olympic na Taipei na kasar Sin. Yanzu, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing yana tuntubar sauran kasashe mambobi sama da 200 na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa kan harkokin rarraba tikitocin shiga.

Jama'a masu saurare, za a gudanar da ayyukan sayar da tikitocin shiga na taron wasannin Olympic na Beijing cikin matakai uku. Mataki na farko shi ne daga yanzu zuwa watan Satumba na wannan shekara, ciki, daga ran 15 ga watan Afrilu zuwa ran 30 ga watan Yuni, lokaci ne na gabatar rokon sayen tikitocin shiga, wato ke nan jama'a na iya gabatar da takardun oda a wannan lokaci; A watan Yuli da watan Agusta, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing zai kidaya takardun odar. Idan tikitocin da aka yi odarsu sun wuce jimlar tikitocin da filaye da dakunan wasanni ke iya sayarwa a hakikance, to za a tabbatar da masu samun tikitocin shiga ta hanyar kada kuri'a kan kamputa. A cikin wannan lokaci, za a yi odar dukan tikitocin shiga na bikin budewa da na rufe taron wasannin Olympic na Beijing, da kuma na kashi 50 cikin kashi 100 na kallon gasanni ga mutane na gida da na waje;

Daga watan Oktoba zuwa watan Disamba na shekarar 2007, mataki na biyu ne na odar sauran kashi 50 cikin kashi 100 na tikitocin shiga na taron wasannin Olympic na Beijing. Daga watan Afrilu na shekarar 2008 har zuwa ranar kammala taron wasannin Olympic na Beijing, mataki na uku ne na sayar da tikitocin shiga.

Mr. Rong Jun,wani jami'in kula da harkokin tikitoci na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana, cewa ko da yake kada kuri'a na kunshe da sa'a, amma jama'a za su fi samun damar karbar tikitocin shiga da suke bukata don nuna sha'awar kallon gasanni.

Jama'a masu saurare, harkokin sayar da tikitocin shiga na taron wasannin Olympic na Beijing suna kuma da wasu halayen musamman. Alal misali: domin daukaka ci gaban yunkurin fadakar da kan matasa da kananna yara a game da ilmin wasannin Olympic, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing musamman ne ya kaddamar da wani tsarin rarraba tikitocin shiga domin tabbatar da tabbatar da " shirin bada ilmi ga matasa da kananan yara" a fannin wasannin Olympic, wato ke nan za a sayar da wasu tikitocin shiga ga 'yan makaratun midil da na firamare da kuma 'yan wasa samari da yara na kasar Sin. Ban da wannan kuma, domin aikata hasashen " taron wasannin Olympic na kore-shar", za a yi amfani da kayayyaki irin na kiyaye muhalli wajen dabin tikitocin shiga; kazalika, kasafin fuskar tikitocin shiga zai ci gaba da bin hasashen kasafi da har kullm ake nuna na taron wasannin Olympic na Beijing, wato ke nan tikitocin shiga za su zama " kayayyakin fasaha" wadanda lallai suke cancantar a adana su.

Jama'a masu saurare, hanya mafi kyau da za a bi wajen shiga harkokin wasannin Olympic ita ce shiga cikin filaye da dakunan wasanni domin kallon gasanni. Saboda haka, aminai masu sha'awar taron wasannin Olympic na Beijing su tashi tun daga yanzu don odar tikitocin shiga na gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing. (Sani Wang)