Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-01 18:52:38    
Ana bunkasa tattalin arzikin lardin Guangdong na Sin cikin sauri ta hanyar bunkasa aikin masana'antu da kasuwanni

cri

Lardin Guangdong da ke bakin teku na kudancin kasar Sin wani lardin kasar Sin ne da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude wa kasashen waje tun can da, haka kuma yana daya daga cikin lardunan kasar Sin da suka fi samun ci gaba a fannin tattalin arziki. A shekarar bara, jimlar kudi da lardin ya samu daga wajen samar da kayayyaki ya kai kudin Sin Renminbi Yuan biliyan 2600, wato ke nan ta dauki kashi 12. 4 cikin dari bisa ta duk kasar Sin. Ka zalika yawan matsakaicin makamashi da ya yi amfani da shi wajen samar da kayayyaki ma ya yi kasa kasa sosai a duk kasar Sin. Lardin Guangdong ya iya samun kyakkyawan sakamako kamar haka, sabo da na cin gajiyar bunkasuwar aikin masana'antu ta fahasar zamani da kyautata kasuwanni.

Ko da yake na'urar shara ba bakon abu ba ne ga jama'a, amma ba safai a kan ga mutum-mutumi mai kwasan shara ba. A gun wani bikin baje koli da aka shirya a birnin Guangzhou a kwanakin baya ba da dadewa ba, an nuna wani irin mutum-mutumi mai kwasan shara. Malama Liu wadda ke yin harkokin farfarganda kan masana'antun kera mutum-mutumin nan ta bayyana cewa, "irin wannan mutum-mutumi mai kwasan shara yana iya gano shara shi da kansa, da ya gano shara, sai ya kwashe ta. Yana iya share shara a wani daki mai fadin muraba'in mita 10 a cikin awa daya. Da ya gama aiki, ya iya zubar da shara shi da kansa, sa'an nan kuma idan ba ya da wutar lantarki, zai iya nemo wurin da ya sake iya samun wutar lantarki."

Wannan mutum-mutumi mai kwasan shara wani sabon kaya ne da wata masana'anta mai zaman kanta ta yi bincikensa da kuma kera shi. Jin kadan bayan gwajin mutum-mutumin, sai ya jawo hankulan jama'a kwarai. Ko da yake farashinsa yana da tsananin tsada, amma an yi ta odarsa sosai daga wurare daban daban na duniya. Babban manajan masana'antar ya bayyana cewa, ta hanyar kirkirowa, sun sami riba mai tsoka.

A can da , Babban Kamfani mai suna "Chuangwei" wata karamar masana'anta ce ta fitar da linzamin sarrafa telebijin, yanzu ya riga ya zama wani babban kamfanin kasa da kasa na kera kayayyakin gida masu aiki da wutar lantarki ta hanyar kirkirawa. Malam Zhang Xuebin, babban jami'in gudanarwa na babban kamfanin yana ganin cewa, bunkasuwar kamfaninsa ta dogara kan masu kirkire-kirkire. Ya ce, "yayin da muka bunkasa kamfaninmu, mun fitar da akwatin telebijin na farko a kasar Sin wanda ya dace da duk hanyoyin waya da ake bi wajen watsa shirye-shiryen telebijin a duniya. Don haka kamfaninmu ya shiga kasuwannin sayar da telebijin mai launi tare da nasara. Yanzu, mun mayar da sabuwar fasaha da kayayyaki na sabon salo bisa matsayin manyan manufofi da muke bi cikin dogon lokaci. Bisa ci gaba da muka samu a cikin shekaru sama da 10 da suka wuce, yanzu kamfaninmu ya riga ya zama wani babban kamfanin kera telebijin mai launi daga wata karamar masana'antar kera linzamin sarrafa telebijin."

A sakamakon ci gaba da ake ta samu wajen daga matsayin masana'antu, lardin Guangdong ya kafa sabbin kasuwannin musamman da ake sayar da kayayyaki ta hanyar zamani. Alal misali, a birnin Guangzhou, fadar gwamnatin lardin, an kafa irin wadannan manyan kasuwanni guda 15 da ake sayar da tufafi da kayayyakin fata da mai da shayi da VCD da sauransu. Malam Mai, wani dan kasauwa ne da ke sayar da tufafi a birnin ya ce, "yawan fufafi da ake dinkawa da farashinsu da kuma ingancinsu na kasuwanninmu suna kan matsayi mai rinjaye a wurare daban daban na kasar Sin. Alal misali, farashin tufafi da 'yan kasuwa suka saya a kasuwanninmu ya yi kasa da na tufafi da ake sayarwa a wuraren da ake dinkinsu. Kazalika ingancinsu da ire-irensu ma sun fi na sauran wurare. Sabo da haka baki suna sha'awar zuwan kasuwanninmu don sayen tufafi. " (Halilu)