Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-06-01 11:10:36    
Rangadin ban kwana na Blair a Afrika

cri

Firaministan kasar Burtaniya Tony Blair ya sauka a birnin Johnnesburg na Afrika ta Kudu jiya Alhamis. Wannan dai zango na karshe ne na rangadinsa a Nahiyar Afrika, kuma ziyara ce ta karshe da yake yi kafin ya yi murabus daga mukaminsa na firaministan kasar. Kafofin yada labarai na Burtniya suna kiran rangadinsa na wannan gami a kan cewa " rangadin ban kwana". Wasu manazarta sun yi hasashen, cewa rangadin ban kwana da Mr. Blair yake yi a Nahiyar Afrika kila zai kasance tamkar wani abu ne mafi muhimmanci da ya gada a duk tsawon zaman rayuwarsu na siyasa tun bayan da kasar Burtaniya ta ci tura bisa manufar da ta aiwatar a kasar Iraki.

Da farko, babban makasudin rangadin Mr. Blair a wannan gami, shi ne kokarin bayyana nasarar da ya cimma a game da manufar da yake aiwatarwa game da harkokin Afrika. Ana tune da, cewa a shekarar 2003, bisa sulhuntawar da firaminista Blair ya yi ne, shugaban kasar Libya Mu'ammar Al-Qadhafi ya yi watsi da shirin nazari da kuma kera makaman kare-dangi yayin da ya dauki alkawarin yaki da 'yan ta'adda. Cimma tudun dafawa da aka yi a kan batun Libya ya zama wani abun misali da aka dauka wajen daidaita batun nukiliyar Korea ta Arewa ,da batun nukiliyar Iran da dai sauran batutuwa. A ran 29 ga watan jiya, Mr. Blair ya fada wa Qadhafi cewa, huldar dake tsakanin kasashen Burtaniya da Libya ta sami sauye-sauye daga doron kasa cikin shekaru 3 da suka shige; kuma dangantakar dake tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya tana ta samun ingantuwa da karfafuwa.

Lallai kasar Burtaniya ta ci gajiyar lamarin. Tuni a farkon shekarar 2004 wato jim kadan bayan da kasar Libya ta yi watsi da shirinta na bunkasa manyan makaman kare-dangi, kamfanin man fetur na Shell na Burtaniya ya samu kwangilar binciko iskar gaz a Libya; Amma duk da haka, mutane da yawa na Libya sun nuna bacin rai saboda jari kalilan ne kasashen Yamma suka zuba a kasarsu.

Bugu da kari, Mr. Blai yana sa ran sa kaimi a karshe ga rukunin kasashe 8 wajen daidaita maganar tallafa wa kasashen Afrika. Idan ba a manta ba, Mr. Blair ya taba yin nasarar janyo hankulan gamayyar kasa da kasa musamman ma kasashe masu hannu da shuni kan maganar fama da talauci da kasashen Afrika ke yi. Ban da wannan kuma, a shekarar 2005, Mr. Bair ya yi kokari matuka wajen shawo kan wasu kasashe don su rattaba hannu kan yarjejeniyar tallafa wa kasashen Afrika, inda aka alkawarta rubanya yawan kudaden da ya kai dola biliyan 50 da za a bai wa kasashen Afrika kafin shekarar 2010, da kuma yafe basussukan da ake bin kasashe 14 mafi talauci na Afrika. Jiya, Mr. Blai ya sake jaddada, cewa idan kasashe masu sukuni ba su cika alkawuran da suka dauka na bada taimakon kudu ga kasashen Afrika ba, to labuddah za a samu barazana wajen gudanar da yunkurin shimfida demokuradiyya da samun wadata a wannan babban yankin Afrrika. Dadin dadawa, Mr. Blair ya yi fatan za a mayar da batun Afrika a matsayin batu na farko da za a tattauna a kai a gun taron koli na rukunin kasashe 8 da za a gudanar a mako mai kamawa.

Ko da yake firaministar kasar Jamus bugu da kari shugabar rukunin kasashe 8 a wannan zagaye Madam Angula Merkel ta bayyana aniyarta ta kalubalantar shugabanni mahalartan taron da su cika alkawuran da suka dauka na tallafa wa kasashen Afrika, amma duk da haka, ra'ayoyin bainal jama'a sun yi shakka kan martanin da za a mayar a game da kalmominta.

Da yake ya kasance da bambancin ra'ayoyi tsakanin kasashe masu hannu da shuni a kan wannan magana da kuma wasu dalilan kasashen Afrika na kansu, shi ya sa aka mayar da yunkurin kawar da talauci a Afrika a matsayin gudun "dogon zango wato Marathon".

Yanzu ana ganin cewa, matsayin da Mr. Blair da kuma magajinsa Mr. Brown suka dauka ya tashi daya a kan wannan magana. Wasu manazarta suna kyautata zaton cewa ba za a canza manufar da za a aiwatar game da harkokin Afrika ba bayan Mr. Brown ya kama ragamar mulkin Burtaniya. Hakan zai bada gudummowa ga rike abun da Mr. Blair ya gada a fannin siyasa. ( Sani Wang )