Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-31 12:55:02    
Garkama takunkumi ba zai amfana wa yunkurin warware batun Darfur na Sudan ba a cewar wani kwararre na kasar Sin

cri

An labarta, cewa shekaran-jiya, shugaba Bush na kasar Amurka ya shelanta, cewa kasarsa ta tsaida kudurin daukar sabbin matakan garkama takunkumi ga kasar Sudan. A lokaci daya, bangaren kasar Amurka ya fayyace, cewa kasar Amurka na yin la'akari da kalubalantar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince da sabon kudurin garkama takunkumi kan kasar Sudan. A nasa bangaren, shugaba Bashir na kasar Sudan ya mayar da martanin, cewa garkama takunkumi da kasar Amurka za ta yi ga kasar Sudan ba zai haifar da komai ba, illa zai janyo mugun tasiri ga yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Darfur. " Amma duk da haka", in ji shi, " matakin da kasar Amurka za ta dauka ba zai dakatar da kokarin da gwamnatin Sudan take yi wajen tabbatar da samun zaman lafiya a wannan yanki ba". To, me ya sa kasar Amurka ta kara daukar tsauraran matakin garkama takunkumi kan kasar Sudan? Shim ko irin mataki zai iya bada amfani ga warware batun Darfur? Wakilinmu ya bakunci Mr. Wang Hongyi, mataimakin daraktan ofishin nazarin harkokin Gabas ta Tsakiya da na Afrika na kasar Sin don jin ta bakinsa a game da wannan lamari. Kwararre Wang Yongyi ya furta, cewa " Wani muhimmin dalilin da ya sa gwamnatin kasar Amurka ta kara garkama takunkumi kan kasar Sudan, shi ne dalilin cikin kasarta yayin da take bayyana aniyar kara matsa lamba ga gwamnatin Sudan ta hanyar garkama takunkumi, wato ke nan kasar Amurka na neman cimma tudun dafawa wajen warware wannan maganar Afrika don lafa zargin da ra'ayoyin bainal jama'a suke yi a game da manufofin diplomasiyya da take aiwatarwa; Dalili daban da ya sa kasar Amurka ta yi haka, shi ne tana so ta kara matsa lamba ga gwamnatin Sudan wajen amincewa da shirin mataki na biyu na na yarjejeniyar zaman lafiya da tsohon babban sakataren MDD Mr. Kofi Annan ya gabatar, wanda ya shafi batun jibge sojoji da kuma manyan makamai; Dadin dadawa, kasar Amurka ta kara daukar matakin garkama takunkumi kan kasar Sudan ne domin tana so ta nuna wa kasashen Turai alamar nemansu da su ci gaba da bin sawunta a kan batun Darfur.

Amma, matakin da kasar Amrka za ta dauka na garkama takunkumi bai samu martani daga sauran bangarori ba. Babban sakatare Ban Ki Moon na MDD ya bayar da wata sanarwa a wannan rana cewa, kudurin kasar Amurka ba ya wakiltar kwamitin sulhun. Ban da wannan kuma, Mr. Liu Guijin, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Darfur shi ma ya bayyna ra'ayinsa, cewa matsa lamba da garkama takunkumi ba za su bada amfani ga daidaita batun Darfur. Kwararre Wang Hongyi ya yi na'am da ra'ayinsa. Ya fadi, cewa: 'Yanzu, gwamnatin Sudan tana tuntubar sauran kasashen duniya yayin da ta amince da shirin da Mr. Annan ya kaddamar da shi bisa manufa. To, kudurin da kasar Amurka ta fito da shi a wannan lokaci, babu tantama ba zai bada amfani ga daidaita wannan magana, musamman ma maganar kyautata huldodin dake tsakanin gwamnatin Sudan, da 'yan tawayenta da kuma 'yan gudun hijira ba ; haka kuma zai haifar da illa ga yin hadin gwiwa da sulhuntawa tsakanin gamayyar kasa da kasa a fannin siyasa da na tattalin arziki dake shafar batun Darfur. Dadin dadawa, matakin Amurka zai kawo cikas ga bangarori daban-daban masu shiga tsakani musamman ma kasar Sin da suke fi taka muhimmiyar rawa mai yakini kan wannan magana.

A karshe dai, darakta Wang Yongyi ya jaddada, cewa : "A zahiri dai, halin da ake ciki yanzu a nahiyar Afrika yana da kyau, wato ke nan sun samu ci gaba mai gamsarwa a fannin siyasa da na tattalin arziki. Kasashen Afrika suna fatan gamayyar kasa da kasa za ta kara karfin daidaita batun Darfur ta hanyar shawarwari cikin lumana, ta yadda za a samu zama mai dorewa a Nahiyar Afrika. ( Sani Wang )