Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-30 18:17:07    
Wani mashahurin mai daukar hotuna na kasar Sin mai suna Deng Wei

cri

Kwanan baya, gidan nuna kayayyakin fasaha na kasar Sin ya soma tanadin hotuna 100 da wani mashahurin mai daukar hotuna na kasar Sin Mr Deng Wei ya dauka. Wannan ne karo na farko da gidan ya yi tanadin hotuna da yawa na wani mai daukar hoto. Mr Deng Wei ya riga ya yi suna sosai a rukunonin masu daukar hotuna na kasashen duniya, a cikin shekaru da yawa, ya kashe kudaden da ke cikin aljihunsa na kansa don je yawon daukar hotuna a ko'ina a duniya, shi ya sa rukunonin masu daukar hotuna na gida da na waje sun ce, aikinsa sabon aiki ne da ya yi a tarihin daukar hotuna na duniya.

Daga cikin hotunan da yawansu ya kai 100 kuma ya mika wa gidan nuna kayayyakin fasaha na kasar Sin a kyauta, da akwai hotunan shahararrun mutane da halin da mutanen farar hula suke ciki da abubuwan da ake yi a cikin zaman rayuwa, kuma rabinsu ne hotunan shahararrun mutane na fannin al'adun kasar Sin da na duniya, ciki har da babban limamin krista kuma wanda ya sami lambar yabo ta Nobel a fannin shimfida zaman lafiya Mr Desmond Mpilo Tutu da tsohon shugaban kasar Amurka Geoge Bush da wata mawallafiyar kasar Britaniya Doris Lessing da tsohon shugaban kasar Singapore Mr Lee Kuan Yew da dai sauransu.An haifi Mr Deng Wei a shekarar 1959 a birnin Beijing na kasar Sin, mahaifinsa yana aiki a fannin al'adu da ba da ilmi, kuma gidansa yana dab da gidajen wasu shahararrun mutane masu aikin al'adu. Tun lokacin da ya ke karami, yana son yin zane-zane, a lokacin da ya cika shekaru 16 da haihuwa, wani mashahurin mai yin zane-zane na kasar Sin Mr Li Keran ya soma koyar masa wajen yin zane-zanen gargajiyar kasar Sin. Bayan shekaru biyu da suka wuce, ya soma koyon ilmin abubuwa masu kyau na hallita da ilmin falsafa na kasashen yamma daga shahararren mai yin nazari kan abubuwa masu kyau na halitta na kasar Sin Mr Zhu Guangqian.

A shekarar 1978, Mr Deng Wei ya shiga sashen daukar hotuna na kolejin koyar da ilmin sinima na birnin Beijing ta hanyar jarrabar da aka yi masa. A farkon lokacin da yi koyon ilmin daukar hotuna, sai ya mayar da malamansa guda biyu bisa matsayin samfurori, sa'anan kuma sauran mutane sun dauki hotunan da ya dauka kwata kwata, saboda haka Mr Deng Wei ya yi tunani cewa, a wancan lokaci, mutanen da suka san samfurorin mutanen al'adu ba su da yawa, amma tunaninsu da abubuwan da suka yi sai mutane da yawa suka karbe su, mutane da yawa kuma suna son ganin samfurorinsu. Saboda haka ina son daukar hotunansu don bayyana su sosai ga jama'a.

Bisa jagorancin mahaifinsa ne, Mr Deng Wei yana daukar hotunan tsofaffin mutanen da yawansu ya kai 100 ko fiye a cikin lokacin hutu, sa'anan kuma wadannan tsofaffin mutane sun mutu bi da bi, hotunansu da Mr Deng Wei ya dauka sun zama hotunan da ba za iya dauka ba a tarihin al'adun kasar Sin, shi ya sa ya sami martani sosai daga rukunonin al'adu da na masana da na fasahohi na kasar Sin. A shekarar 1986, karo na farko ne Hongkong ya buga littafin gabatar da mutanen al'adun kasar Sin na farko, ba da dadewa ba, Mr Deng Wei ya sami lambobin yabo da yawa.

Mahaifinsa da malaminsa Li Keran sun mutu bi da bi, Mr Deng Wei ya yi bakin ciki sosai da sosai, har ma ya kamu da ciwo mai tsanani. Bayan da ya sami sauki, sai ya tsai da kudurin aiwatar da shirin da mahaifinsa ya tsara masa na daukar hotunan shahararrun mutanen duniya, ya tafi kasar Britaniya, ya sha wahaloli da yawa, amma a cikin shekaru da yawa da suka wuce, ya riga ya manta su kusan dukka, amma ya tuna sosai da wani zaman alheri da ya samu a cikin mawuyacin hali , wato ya sami wata damar yin barci a kan wani gado, ya ce, a wancan daren, na yi barci sosai, da na kwanta a kan gado, tamkar yadda na soma sanin abun da na ke kwanta a kai da cewar wai gado ke nan.

Mr Deng Wei ya bayyana cewa, kafin daukar hoto na wani mashahurin mutum, dole ne ya shirya abubuwa da yawa, Kamar littafin da aka rubuta dangane da tarihin mutumin da littattafan da ya wallafa da dai saruansu. Ya ce, lokacin da na je daukar hoto na babban limamin krista Mr Tutu, sai na rubuta kalmomin a kan Passport da cewa, Mr Deng Wei ya je kasar Afrika ta Kudu don daukar hoto na babban limanin krista Mr Desmond Mpilo Tutu, da Mr Tutu ya ga wannan sai ya yi farin ciki sosai. (Halima)