Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-30 18:12:34    
Bayani game da mutumin nan da aka ce ya fi kowa tsawo a duniya a halin yanzu

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Yakubu Mohammed Rigasa, mazaunin jihar Kaduna da ke tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya turo mana, ya ce, ina so ku kara mini bayani game da mutumin nan da aka ce ya fi kowa tsawo a duniya a halin yanzu.

To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu ba ku tarihin mutumin nan da ake kiransa "Bao Xishun", wanda ke da tsayin mita 2.36, har ma ya kasance mutumin da ya fi tsayi a duniya a halin yanzu.

Masu sauraro, a jihar Mongoliya ta gida da ke arewacin kasar Sin, akwai wani mutum mai suna Bao Xishun, wanda ya fito daga wani iyali na makiyaya. A lokacin da yake da shekaru 15 da haihuwa, ba zato ba tsamani sai ya fara girma ya yi ta kara tsayi kwarai da gaske, a lokacin da shekarunsa ya kai 20 da haihuwa, sai tsayinsa ya kai mita 2.1.

Amma Bao Xishun bai ji dadi ba, a maimakon hakan kuma, yana damuwa. Sabo da ya fi saura iya ci, duk inda ya tafi, babu gadon da zai iya kwantawa, kuma da ya fita daga gida, a kan yi ta kallonsa. A lokacin, Malam Bao Xinshun ya taba zuwa wurin likita, don a yi masa bincike. Amma bisa binciken da aka yi masa, ban da dan ciwon gwiwa da aka gano, kome lafiya lau. A lokacin kuma, tsayinsa ya jawo hankalin wani malamin horar da 'yan wasan kwallon kwando, har ma malamin ya gayyace shi zuwa kungiyar 'yan wasan kwallon kwando. Bao Xishun yana murna ya shiga horaswa. Amma abin bakin ciki shi ne, kome kokarinsa, kafafuwansa ba su iya jurewa gasa mai tsanani da ake yi a fagen wasan kwallon kwando. Sabo da haka, bayan shekaru biyu, ba yadda ya iya yi sai ya koma gida.

Amma duk da haka, a watan Satumba na shekarar 2004, wani dan kasuwa da ke gudanar da wani dakin cin abinci ya ji labarin malam Bao Xishun, sai ya je gidansa, don gayyace shi da ya zama wata alama mai wakiltar dakin cin abincinsa da ke garin Chifeng da ke gabashin jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin, kuma Bao Xishun ya yarda.

Zuwan malam Bao Xishun ke da wuya, a cikin 'yan kwanaki ne kawai sai hada-hadar harkokin dakin cin abincin suka fara gudana sosai da sosai, jama'a na zuwa dakin cin abinci, don kallon wannan mutum mai tsayin gaske. Hakan nan kuma, Bao Xishun ya fara yin suna kwarai da gaske.

A karshen shekarar 2004 kuma, bisa taimakon da kafofin yada labarai suka ba shi, Bao Xishun ya yanke shawarar neman sa sunansa a cikin kundin Guinness na sunayen mutanen da suka shahara a duniya, kuma a matsayin mutumin da ya fi tsayi. A watan Yuli na shekarar 2005 kuma, bisa binciken da aka yi wa jikinsa, hedkwatar kula da kundin Guinness na sunayen mutanen da suka shahara a duniya tana ganin cewa, Bao Xishun yana da lafiya, shi ya sa ya ba shi takardar shaida a matsayin mutumin da ya fi tsayi a duniya wanda kuma tsawonsa na hallita ne.(Lubabatu)