Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-30 08:29:58    
'Yar wasa daga kasar Sin Chen Zhong ta zama zakarar wasan karate ta gasar fid da kwanin duniya

cri

Masu sauraro,kwanakin baya ba da dadewa ba,an kammala gasar fid da gwanin duniya ta wasan karate ta shekarar 2007 a birnin Beijing na kasar Sin,kungiyar `yan wasan kasar Sin ta samu lambobin zinariya biyu da lambar tagulla daya,wato ta samu sakamako mafi kyau da ba ta taba samu a tarihi ba.A gun gasar da aka shirya a rana ta karshe,shahararriyar `yar wasa daga kasar Sin wadda ta taba zama zakarar taron wasannin Olimpic sau biyu Chen Zhong ta samu lambawan a gun gasar aji na sama da kilo 72,daga nan kuma ana iya cewar ta samu cikakkiyar nasara.Dalilin da ya sa haka shi ne domin Chen Zhong ta samu dukkan zakaran wasan karate na taron wasannin Olimpic da gasar cin kofin duniya da kuma gasar fid da gwanin duniya.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

`Yar wasan karate Chen Zhong ta yi suna sosai a duk fadin duniya,yanzu dai tana da shekaru 25 da haihuwa.Kafin wannan,Chen Zhong ta taba samun lambobin zinariya biyu na wasan karate a gun taron wasannin Olimpic,ban da wannan kuma ta taba samun lambar zinariya daya ta gasar cin kofin duniya da lambar zinariya daya ta taron wasannin Asiya,amma ba ta taba zama zakarar gasar fid da gwanin duniya ba.A gun wannan zama na gasar fid da gwanin duniya da aka shirya a birnin Beijing,kodayake tana jin ciwon raunin da ta samu daga wasa,amma ta lashe abokan gaba ta shiga gasa ta karshe da sauki.A gun gasar karshe,ta yi kokari ta lashe `yar wasa daga kasar Korea ta kudu Han Jin Sun ta zama zakara.Bayan gasa,Chen zhong ta rufe jikinta da tutar kasar Sin ta gudu a kewayen filin wasa domin nuna godiya ga `yan kallo.Chen Zhong ta gaya wa manema labarai cewa,  `Na zama zakarar gasar fid da gwanin duniya a garina wato Beijing,wannan yana da ma`anar musamman,ina jin dadi saboda na yi kokari kuma na ci nasara.`

Babban sakataren kungiyar wasan karate ta kasar Sin Zhao Lei ya bayyana cewa,a kullum Chen Zhong ta yi iyakacin kokari,ana iya cewar dalilin da ya sa Chen Zhong ta ci nasara shi ne domin ta yi kokari ba dare ba rana.Chen Zhong ta fara koyon wasan karate a shekarar 1995,a shekarar 1997,ta shiga kungiyar wasan karate ta kasar Sin.Kawo yanzu,shekaru goma sun wuce.Mr.Zhao Lei ya ce: `Tsawon lokacin horon sana`a yana da muhimmanci kwarai da gaske ga `yan wasan sana`a,lokacin horon sana`a na Chen Zhong ya fi sauran `yan wasan kungiyar `yan mata tsawo,shi ya sa ta fi sauran `yan wasa gwaninta a fannoni daban daban,alal misali fasaha da tunani da kuma halin gasa.`

Mamar Chen Zhong Zhang Meiying ta gaya mana cewa,diyarta ta taba jin rauni sau da yawa yayin da take wasa,kowace rana tana fama da ciwon da raunin wasa ya kawo mata,amma ba ta daina yin kokari ba.Zhang Meiying ta ce,a idonsu wato a idon iyalanta,Chen Zhong ita ce wata karamar yarinya kawai,abincin da ta fi son ta ci shi ne taliyyar kwai da mamarta ta dafa.

Wu Jingyu,`yar wasa daban daga kasar Sin wadda ta samu lambar zinariya ta farko a gun wannan zama na gasar fid da gwanin duniya ita ma ta bayyana cewa,ba ma kawai Chen Zhong ita ce wata `yar wasan tauraro ba,har ma ita ce `yar uwarta.Daga shekarar 2005,wato bayan Wu Jingyu ta shiga kungiyar kasar Sin a wannan shekara,sai sun fara yin zaman rayuwa a cikin daki daya.Wu Jingyu ta ce:  `A kullum ina mayar da Chen Zhong abin koyina,ita ma tana kula da mu tana kaunarmu.`

Wu Jingyu ta gaya mana cewa,Chen Zhong ta taba gaya mata sau tarin yawa cewa,abu mafi muhimmanci ga `yan wasan kungiyar kasa shi ne su yi kokari bisa karfin kansu,kamata ya yi su yi cudanya da sauransu mutane,dabara mafi dacewa ita ce sabbin `yan wasa su tambaye malaman koyarwa da tsoffin `yan wasa yadda za su warware wahalhalun dake gabansu,daga baya kuma za su daga matsayinsu daga duk fannoni.

Yanzu dai Chen Zhong ta riga ta zama lambawan a gun dandalin wasan karate na duniya,amma ba ta nuna girman kai ba,sai ta ci gaba da sanya matukar kokari domin shiga taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekara mai zuwa.Chen Zhong ta ce,ko shakka babu za ta yi kokari kamar yadda ta yi a da,tana fatan za ta ci gaba da zama zakarar taron wasannin Olimpic wato ta hau kan dandalin zakara a bakin kofar gidanta.Ana fatan Chen Zhong za ta cim ma burinta.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)