Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-30 08:28:38    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (23/05-29/05)

cri

Ran 27 ga wata,agogon wurin,a babban birnin kasar Croatia,an kammala zama na 49 na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur wadda aka shafe kwanaki 7 ana yinta.`Yan wasa daga kasar Sin sun samu dukkan lambobin zinariya da na azurfa na gasanni biyar.Wannan shi ne karo na 6 da kungiyar kasar Sin ta samu dukkan zakaru na gasanni biyar,kuma shi ne karo na 3 da ta samu dukkan lambobin zinariya da na azurfa na gasanni biyar.Wang Liqin ya zama zakaran gasar maza,Guo Yue ta zama zakarar gasar mata,Wang Nan da zhang Yining sun zama zakarun gasar dake tsakanin mata biyu biyu,Ma Lin da Chen Qi sun zama zakaran gasar dake tsakanin maza biyu biyu,ban da wannan kuma Wang Liqin da Guo Yue sun zama zakarun gasa ta gaurayawar namiji da mace.

Ran 22 ga wata,an kammala gasar fid da gwanin duniya ta wasan karate a birnin Beijing na kasar Sin.A gun gasar da aka yi a rana ta karshe,`yar wasa daga kasar Sin Chen Zhong wadda ta taba zama zakarar taron wasannin Olimpic sau biyu ta zama zakara ta gasa ta mata ta aji na sama da kilo 72,daga nan kuma ta samu dukkan zakarun wasan karate na taron wasannin Olimpic da gasar cin kofin duniya da kuma gasar fid da gwanin duniya.Kawo yanzu,an kammala dukkan gasannin wannan zama na gasar fid da gwanin duniya,kungiyar kasar Sin ta samu lambobin zinariya biyu da na tagulla daya.

Ran 27 ga wata,an kammala gasar shahararrun `yan wasa ta wasan kwallon boli ta duniya ta kasar Sin ta shekarar 2007 a birnin Wu Xi dake gabashin kasar Sin,kungiyar kasar Sin ta zama zakara.

Ran 23 ga wata,kunigyar wasan kwallon kafa ta kasar Italiya wato AC Milan ta lashe kungiyar Liverpool ta kasar Ingila da 2 bisa 1,ta zama zakara,wannan shi ne karo na 7 da kungiyar AC Milan ta zama zakaran hadaddiyar gasar zakaru ta Turai.(Jamila zhou)