Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-29 21:27:46    
Ainihin batun Darfur shi ne batun neman samun bunkasuwa, in ji kasar Sin

cri
A gun taron manema labaru da aka yi a nan Beijing, a ran 29 ga wata, Liu Guijin, wakilin gwamnatin kasar Sin mai kula da batun Darfur, ya bayyana cewa, dalilan da ya haddasa rikicin Darfur shi ne domin kabilu daban daban sun kwace ruwa daga kogi da yankuna a sakamakon rashin ci gaba da talauci da kuma karancin albarkatun kasa, anihin wannan batu shi ne batun neman samun bunkasuwa.

Mr. Liu ya kara da cewa, matsa lamba da garkama takunkumi ba za su yi amfani a fannin warware rikicin Darfur. Ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su yi amfani da hanyar siyasa da kuma hikima domin warware rikicin Darfur cikin ruwan sanyi.

Mr. Liu Guijin ya kai wa kasar Sudan ziyara tun daga ran 19 zuwa ran 23 ga watan Mayu. Ya fayyace cewa, ya samar da damuwar da kasashen duniya ke nuna wa gwamnatin Sudan kan batun Darfur, ya kuma yi kira ga gwamnatin Sudan da ta rubanya kokari wajen gaggauta shimfida zaman lafiya a kasar.

Mr. Liu ya ci gaba da cewa, gwamnatin Sin ta bai wa yankin Darfur da kungiyar musamman ta Majalisar Dinkin Duniya taimakon kayayyaki da kyautar kudi na jin kai, wadanda darajarsu ta kai misalin dalar Amurka miliyan 10 don rage matsalar taimakon jin kai da ake fama da ita a wannan yanki. Ban da wannan kuma, don goyon bayan gudanar da shirin da ke kunshe da matakai 3 da Kofi Annan, tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar, kasar Sin za ta tura sojoji masu aikin injiniya 275 zuwa Sudan don gudanar da aiki na mataki na 2.(Tasallah)