Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-29 19:23:18    
Kasar Sin za ta hana shan taba sigari a wuraren jama'a

cri

A ran 29 ga wata, jami'an ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin sun bayyana a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin aiwatar da "Yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba sigari", yanzu tana da shirin gyara "Ka'idojin kula da harkokin kiwon lafiya a wuraren jama'a". Bisa sabbin ka'idojin da za a bayar, za a kara hana shan taba sigari a wuraren jama'a. A waje daya, kasar Sin za ta dauki matakin "Hana shan taba sigari a gun gasar wasannin motsa jiki ta Olympics" lokacin da ake shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics a nan Beijing a shekarar 2008. Bugu da kari, za a sanar da ilmi hana shan taba sigari ga jama'a.

Za a kara mai da hankali kan aikin hana shan taba sigari ta hanyar kafa dokoki, wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ke dauka lokacin da take hana shan taba sigari. Madam Yang Gonghuan, mataimakiyar direktar ofishin ba da jagoranci wajen aiwatar da "Yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba sigari ta kasa da kasa" ta ce, "Kafa dokoki muhimmin mataki ne wajen hana shan taba sigari a wuraren jama'a. Mun ga a sauran kasashen duniya, bayan da aka soma aiwatar da dokokin hana shan taba sigari a wuraren jama'a, a bayyane ne yawan mutanen da suke shan taba sigari a wuraren jama'a yana ta raguwa sosai."

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan mutanen da suke shakar hayakin taba sigari sakamakon taba sigarin da iyalansu ko sauran mutane suke sha ya kai miliyan 540, daga cikinsu mutane fiye da dubu dari 1 sun mutu. Ko da yake ya kasance da ka'idojin hana shan taba sigari a wuraren jama'a a cikin dokoki masu dimbin yawa, amma har yanzu babu wata doka musamman ta hana shan taba sigari a wuraren jama'a a kasar Sin. Bisa sakamakon binciken da aka yi, an ce, kafa wata dokar hana shan taba sigari a wuraren jama'a ya riga ya zama ra'ayin yawancin jama'a na kasar Sin. Alal misali, bisa binciken da aka yi a birane 7 ciki har da birnin Beijing, an ce, mutanen da suka karbi binciken da aka yi musu kuma yawansu ya kai kashi 90 cikin kashi dari sun nuna goyon bayan kafa dokokin hana shan taba sigari a wuraren jama'a, kamar su jiragen kasa da na sama da motocin bus masu sufurin jama'a da makarantu da asibitoci. Mutanen da yawansu ya kai kashi kusan 50 cikin kashi dari sun yarda da a hana shan taba sigari a dakunan cin abinci da na shan giya.

Mr. Wang Longde, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin ya ce, "Kasar Sin kasa ta farko ce da za ta shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics bayan da aka soma aiwatar da 'yarjejeniyar ka'idojin kayyade taba sigari ta kasa da kasa". Sabo da haka, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta yi kira ga biranen da suke shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics za su iya tsara matakan tabbatar da babu taba sigari a gun gasar wasannin motsa jiki ta Olympics, kuma za su iya aiwatar da wadannan matakai a kai a kai. Muna fatan za a iya samar da muhallin yin aiki da wuraren jama'a masu tsabta inda ba za a sha taga sigari ba."

An bayyana cewa, lokacin da ake yin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing a shekarar 2008, za a hana shan taba sigari da nune-nunen tallace-tallacen taba sigari a gun dukkan filaye da dakunan gasar wasannin motsa jiki ta Olympics. A waje daya, birnin Beijing yana da shirin kayyade shan taba sigari a dakunan cin abinci. Bugu da kari kuma, kafin watan Yuni na shekarar 2008, za a hana shan taba sigari a otel-otel da suke da nasaba da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing da dakunan motsa jiki na gasar da dakunan abinci na wuraren kwana na 'yan wasannin motsa jiki da za su halarci wannan gasar. Tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya riga ya soma aiwatar da dokar hana shan taba sigari a wuraren jama'a da ofisoshi.

Mr. Cris Tunon, wani jami'in hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa ya bayyana cewa, hukumar za ta nuna wa kasar Sin goyon baya wajen shirya wata gasar wasannin motsa jiki ta Olympics inda babu taba sigari. "Kasar Sin ta riga dauki alkawarin shirya wata gasar wasannin motsa jiki inda babu taba sigari. Wannan gasa wata muhimmiyar dama ce ga kasar Sin wajen hana shan taba sigari a wuraren jama'a. Gwamnatin kasar Sin ta riga ta tsara shirin yin yaki da taba sigari. Hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa tana fatan za ta iya samar da taimako ga gwamnatin kasar Sin domin cin nasara a gun wannan mihimmin yaki." (Sanusi Chen)