Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-29 19:01:07    
Kololuwar babban dutsen Victoria

cri

Assalamu alaikum. Jama'a masu sauraro. Barkanku da war haka. A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu n ayau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan kololuwar babban dutsen Victoria, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, sauraran kide-kiden gargajiya na kasar Sin a gidan ajiye kayayyakin gargajiya na Henan.(music)

Watakila yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin shi ne birnin zamani mafi kyau gani a duk duniya. dogayen gine-ginen ofisoshi da dagayen manyan benaye da kuma sassan benayen gidajen kwana su ne suke zagaye da kyakkyawar tashar jiragen ruwa, daga can nesa kuma ga tsaunuka a Kowloon. Ko dare ko rana kuma, babban dutsen Victoria a bayyane yake a ko da yaushe masu yawon shakatawa suna kai ziyara ga babban dutsen Victoria mai tsayin misalin mita 554.

Hanya mafi kyau wajen isa kololuwar babban dutsen Victoria ita ce shiga cikin motar dogo, wanda wani irin jirgin kasa ne na musamman mai dogon tarihi. Ya fi kyau ka sami wata kujera a layi na gaba a bangare na dama a cikin wannan motar dogo. Bayan da more ido da manyan gine-gine da kyawawan wurare masu ni'ima a tashar jiragen ruwa daga wannan kujera, ba a iya sifanta yadda a ji ba, sai a ja numfashi. Wasu masu yawon shakatawa su kan shiga cikin motar dogo ta farko da sassafe don gudun rububin mutane da kuma jin dadin kallon ni'imtattun wurare cikin kadaici. Idan kana son ka more idanunka da mi'imtattun wurare mafi kyan gani a Hong Kong cikin sauri, to, kada ka manta da irin wannan motar dogo ta musamman. An fara aiki da ita tun daga shekara ta 1888, wadda ta isa tashar karshe mai tsayin mita 373 a babban dutsen Victoria a cikin mintoci misalin 8 kawai. Motar dogo ta kan fara aiki tun daga karfe 7 da safe zuwa tsakiyar dare a cikin ko wadanne mintoci 15 a ko wace rana.

A kusa da tashar karshe ta motar dogo, wata hasumiya ta samar da baranda da kuma sauran abubuwa masu ban sha'awa ga masu yawon shakatawa. Wani babban gini da ke makwabtaka da ita shi ne babban shago na sayayya da ke cikin wuri mafi tsayi a duk birnin, masu yawon shakatawa suna iya cin abinci a cikin baranda, inda suke iya kallon dukkan tashar jiragen ruwa daga nesa, ko kuma suna cin abinci cikin dakunan cin abinci, inda suke iya kallon kyawawan wurare masu ni'ima duka. Bayan an ketare wata hanya, masu yawon shakatawa sun shiga wani gida gahawa da ke cikin wani gini, wanda a da wata tasha ce da aka samar da kujeru irin na sedan.

To, jama'a masu sauraro. Muna muku godiya da saurarenmu, kuma muna fatan za ku ci gaba da sauraren shirin nan na yawon shakatawa a kasar Sin.