Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, shan lemo kullum zai iya yin illa ga hakoran dan Adam, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, Kasar Sin za ta aika da likitoci masu yawa zuwa kauyuka domin ba da ayyukan hidima. To, yanzu ga bayanin.
A kwanan nan, manazarta na jami'ar south Illinois ta kasar Amurka sun gano cewa, mai yiyuwa ne shan lemo kullum zai iya lalata sinadarin enamel da ke kan hakora.
An bayar da wannan sakamakon nazari ne a kan mujallar ilmin hakora na jama'a ta kasar Amurka. Manazarta na jami'ar sun gudanar da wani gwaji kan yadda lemon kwalba ko na gwangwani ke lalata hakora. Manazarta sun sayi ire-iren lemon sha guda 20 kamar Coka Cola da Pepsi Cola da dai sauransu. Bayan da aka bude su, sai nan da nan aka auna yawan sinadarin acid da ke cikinsu, daga baya kuma an fere enamel daga hakoran da aka cire ba da jimawa ba. Bayan da aka auna nauyinsu, sai a ajiye su a cikin lemon sha, kuma bayan awoyi 48, an fitar da su daga lemon sha don sake auna nauyinsu.
Sakamakon nazarin ya bayyana cewa, yawan nauyin enamel da ke cikin lemon sha iri 7 ya ragu fiye da kashi 5 bisa dari.
Manazarta sun nuna cewa, ko da yake ba za a ajiye lemon sha a cikin baki har kwanaki biyu ba kamar yadda aka yi a cikin gwaji, amma wasu lemon sha sun fara lalata hakora tun lokacin da aka fara shansu, kuma a kwana a tashi, lalatawar hakora za ta kara tsananta.
Sabo da haka manazarta sun ba da shawara cewa, ya fi kyau a yi amfani da tsinke lokacin da ake shan lemo, ta yadda za a iya rage hadarin da ke tsakanin lemo da hakora. Ban da wannan kuma ya fi kyau a sha lemo lokacin da ake cin abinci.
Idan hakora suka lalace, su kan yi zafi. Wani sakamakon nazarin da kasar Sweden ta yi ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne zafin hakora wata alamar farko ce ta kamuwa da cutar zuciya. Kuma yiyuwar samun wannan alama ga mata ta kara da kusan kashi 40 bisa dari idan an kwatanta da maza.
Bisa labarin da wata jarida ta kasar Sweden ta bayar a ran 23 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, an ce, manzarta na jami'ar Umea ta kasar sun gudanar da wani bincike ga mutane 186 da suka kamu da cutar zuciya domin su nuna kayayyakin jiki da suka ji zafi kafin barkewar cutar zuciya. Kuma mutane 71 daga cikinsu sun bayyana cewa, sun taba jin zafin hakora, kuma yawancinsu mata ne. Wasu mutane kuma sun taba ganin likita wajen lafiyar hakora kafin barkewar cutar zuciya, amma likitoci ba su gano ainihin dalilin zafin hakora, daga baya kuma an dauke su zuwa sashen kula da cuttuttukan cikin jikin dan Adam, sai a gano cewa, sun kamu da cutar zuciya.
Ban da wannan kuma manazarta sun nuna cewa, bai kamata ba a dauka cewa idan ana jin zafin hakora, wata alama ce ta kamuwa da cutar zuciya. Amma idan ana jin zafin hakora na dukkan gefuna biyu, kuma zafin yana kara tsananta yayin da ake ci abinci, to ya kamata a mai da hankali kuma ya je asibiti domin ganin likita nan da nan.
Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, Kasar Sin za ta aika da likitoci masu yawa zuwa kauyuka domin ba da ayyukan hidima.
|