Har kullum ana mai da hankali sosai kan abinci da ruwan sha da aikin jiyya da kuma ingancin jini a kasar Sin, haka kuma yanzu gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai kan kula da aikin kiwon lafiya wanda yake da nasaba da wadannan batutuwan da muka ambata a baya. A kwanan nan, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Chen Xiaohong ya yi bayani a birnin Beijing, cewa za a kara aiwatar da dokoki a kan al'amuran da ke jawo hankulan fararen hula a fannonin kiwon lafiya da aikin jiyya domin tabbatar da kiyaye hakkin fararen hula a fannin kiwon lafiya. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan batu.
Tare da bunkasuwar sha'anin kiwon lafiya na kasar Sin, bisa matsayinta na wani muhimmin kashi na sha'anin, aikin sa ido kan ayyukan kiwon lafiya ya samu bunkasuwa sannu a hankali. Yanzu ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta riga ta kafa wata hukumar musamman domin kula da wannan aiki, wato cibiyar sa ido kan ayyukan kiwon lafiya, da kuma ingantawa da raya tsarin sa ido kan ayyukan kiwon lafiya a duk fadin kasar. A cikin wadannan shekaru 3 da suka gabata, a yankunan da ke tsakiya da kuma yammacin kasar Sin kawai, gwamnatin kasar ta kebe kudin Sin yuan biliyan 1.2 wajen inganta ayyukan da hukumomin sa ido kan ayyukan kiwon lafiya na yankunan suka yi. A kwanan nan, a gun wani taron da aka yi a birnin Beijing, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Chen Xiaohong ya yi bayani kan yadda ake tafiyar da ayyukan sa ido kan ayyukan kiwon lafiya a wasu muhimman fannoni. Kuma ya bayyana cewa, "An samu sakamako mai kyau a cikin ayyukan yaki da harkokin yi wa wadanda suke fama da cututtuka jiyya ba bisa doka ba, sa'an nan kuma an kara sa ido kan ingancin jini domin ba da tabbaci ga fararen hula wajen yin amfani da jini ba tare da hadari ba. Ban da wannan kuma an samu ci gaba wajen yaki da cin hanci da rashawa a fannin sayar da magunguna."
Yayin da ake sa ido kan sana'o'in aikin likitanci da muka ambata a baya, gwamnatin kasar Sin ta kara karfi wajen kula da ingancin abinci da aikin kiwon lafiya na 'yan kwadago. Ko da haka, amma sabo da ba a iya gudanar da ayyuka kamar yadda ya kamata lokacin da kasar Sin take canja tsarin tattalin arziki daga tsarin shiri zuwa bisa na kasuwanni, shi ya sa ana kwasancewar matsalar rashin sa ido kan ayyukan kiwon lafiya kamar yadda ya kamata. Alal misali, al'amuran cin abinci mai guda ya kan faru a wasu wurare, kuma ba a iya samun ruwan sha mai tsabta a wasu wurare.
Game da wadannan batutuwa, Mr. Chen ya bayyana cewa, za a aiwatar da dokoki a tsanake domin tabbatar da aiwatar da ayyukan sa ido kan ayyukan kiwon lafiya yadda ya kamata. Kuma ya kara da cewa, "Ya kamata mu mayar da aikin kiyaye hakkin lafiyar fararen hula a matsayin babban tushen ayyukan sa ido kan kiwon lafiya, da kuma aiwatar da ayyukan sa ido kan kiwon lafiya bisa doka. Haka kuma za mu kara aiwatar da dokoki a kan al'amuran da ke jawo hankulan fararen hula a fannonin kiwon lafiya da aikin jiyya domin yaki da laiffuffukan da ke yin illa ga lafiyar fararen hula. "
Haka kuma Mr. Chen ya yi bayanin cewa, a shekarar nan da muka ciki, muhimman ayyukan sa ido kan kiwon lafiya a fannin ba da hidima wajen aikin jiyya su ne, yaki da wadanda suke aikin likitanci ba bisa doko ba, da sa ido kan ingancin jini, da kuma yaki da cin hanci da rashawa a fannin sayar da magunguna.
Ban da wannan kuma a fannin kiwon lafiyar jama'a, kasar Sin za ta sanya ido kan abincin kauyuka da danyun kayayyaki wajen samar da abinci da abin sha da kuma magungunan ba da kariya ga lafiyar jiki da dai sauransu.
Wakilinmu ya samu labari cewa, yanzu ana tafiyar da ayyuka bisa shirin da aka tsara a wadannan fannoni biyu a wurare daban daban na kasar Sin. Alal misali, lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin yana dora muhimmanci kan ayyukan jiyya da tabbatar da ingancin jini. Zhao Lianzhou, wani jami'i a ofishin sa ido kan ayyukan kiwon lafiya na lardin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Lardinmu yana tsayawa tsayin daka kan yaki da tashoshin samun jini ba tare da bisa doko ba. Kuma yanzu mu kan yin bincike da kuma dudduba ingancin jini domin ba da tabbaci wajen samun jini yadda ya kamata."
Haka zalika, mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Chen Xiaohong ya bayyana cewa, yanzu tsarin sa ido kan ayyukan kiwon lafiya na kauyukan kasar Sin ba ya samu kyautatuwa sosai, kuma kwarewar masu sa ido kan ayyukan kiwon lafiya wajen aiki ba ta da kyau, shi ya sa za a mai da hankali a kan kyautata wadannan matsaloli a nan gaba. Kande Gao)
|