Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-28 12:27:32    
Shugaban kwamitin dindindin na majalisar dokoki ta kasar Sin ya samu cikakkiyar nasarar ziyarar kasashe uku.

cri

Jama'a masu sauraro assalam alaikum,barkanku da war haka,barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shirin namu na Duniya Ina labari.A yau za mu karanta wani bayanin da aka ruwaito mana kan ziyarar da shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Wu Bangguo ya kai a kasashen Massar da Hungary da kuma Poland daga ran 18 zuwa ran 27 ga watan Mayu da muke ciki. Shugaban majalisar ya yi wannan ziyarar sada zumunta ne bisa gayyatar da aka yi masa.Mataimakin sakatare janar na kwamitin dindindin na majalisar dokoki na kasar Sin Cao Weizhou wanda ya rufowa Wu Bangguo baya gun ziyarar, ya bayyana cewa wannan ziyara ta kara tabbatar da sakamakon da taron koli na Beijing ya samu cikin tattaunawar fadi albarkacin baki kan hadin kai tsakanin Sin da Afrika,haka kuma ta kara amincewar juna a fannin siyasa tsakanin Sin da kasashe uku da ya ziyarta da kuma tabbatar da muhimman fannoni da hanyoyi kan hadin kan bangarori biyu a tattalin arziki da ciniki da kara mu'amalar zumunta tsakanin majalisar dokoki ta kasar Sin da majalisun na kasashen uku.

A ran 27 ga wata a kan hanyarsa ta komawa gida bayan kammala ziyarar Mr Cao Weizhou ya yi bayani kan wannan ziyara ta shugaban majalisar Wu Bangguo.Ya bayyana cewa ziyarar da shugaban majalisar dokoki ta kasar Sin Wu Bangguo ya yi a Hungary da Poland,ita ce ta farko a kasashen nan biyu,haka kuma ita ce ziyarar ta farko a Massar bayan shekaru 12,sannan kuma wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka kan harkokin waje game daAfrika da Turai.

Duk domin inganta zumucin al'ada dake tsakanin Sin da kasashen uku da ciyar da muhimmiyar dangantakar abokantaka ta tsakanin Sin da Massar da kuma dangantakar abokantaka ta hadin kan aminci ta tsakanin Sin da Hungary da Poalanda gaba, tare da la'akari da halin da kasashen uku ke ciki,Mr Wu Bangguo ya yi musayar ra'ayi da shuabannin Massar kan huldar ta tsakanin bangarori biyu da sauran batutuwa na duniya da yankuna da suka jawo hankulansu gaba daya a kasar Massar;Ya tattauna sosai da shugabannin Hungary musamman kan bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Hungari da hadin kai tsakanin Sin da Turai.A kasar Poland duk inda ya sa kafa,Wu Bangguo ya yi bayani kan matsayin da kasar Sin ta dauka da kuma ra'ayinta kan kan matsaloli na Taiwan da Tibet da kuma hakkin Bil Adama.Shugabanni na kasashen uku da ya ziyarta sun nanata cewa sun nace ga bin manufar Sin daya da yin adawa da "yancin Taiwan" da kuma nuna goyon bayansu kan tabbatar da dinkuwar kasar Sin ta hanyar lumana.Bangarori biyu gaba daya suna fatan kara tattaunawa da sulhuntarwa cikin harkokin duniya domin kare moriyar tarayya.

Mr Cao Weizhou ya ce Massar muhimmiyar kasa ce a Afrika da kuma duniyar larabawa,kuma kasa ce ta farko da ta kulla huldar jakadanci da sabuwar kasar Sin a Afrika da kasashen Larabawa.Makasudin ziyararsa a wannan gami shi ne a kara tabbatar da ra'ayi bai daya da shugabanni na Sin da na Afrika suka cimma daidaito a kai a taron koli na Beijing cikin tattaunawar hadin kan kasar Sin da Afrika da ya gudana a watan Nuwanba na bara da kuma kara kokarin tabbatar da sakamakon da aka samu a taron koli na Beijing.

A lokacin da yake ziyara a kasar Massar Mr Wu Bangguo ya ba da jawabi mai muhimmanci a taron hadin kan kasar Sin da Afrika wajen masana'antu inda ya bayyana sabon cigaban da aka samu wajen tabbatar da manufofin hadin kai masu amfani da gwamnatin kasar Sin ta dauka,kan halin da ake ciki ya gabatar da fannonin hadin kai da hanyoyin sabunta hadin kai da kuma matakan da za a dauka wajen kyautata yanayin hadin kai duk domin karfafa hadin kan masana'antun na kasar Sin da na kasashen Afrika.Ya jadadda cewa kasar Sin za ta ci gaba da hada kanta da kasashen Afrika wajen tabbatar da sakamakon taron koli na Beijing na tattaunawar hadin kan kasar Sin da Afrika,ta sanya kokari wajen hadin kan masana'antu da manyan masana'antun da ke iya samun cigaban kasa,haka kuma zata karfafa hadin kai dake tsakaninta da kasashen Afrika wajen aikin gona da gina manyan ayyuka da fannin masana'antu ta hanyar kafa wurin hadin kan tattalin arziki da cinikayya,da wurin musamman na masana'antu da kuma cibiyoyin ba da misalin koyo a fannin aikin gona ta yadda za su iya samun wadatuwa da cigaba tare.

Lokacin da yake ganawa da shugabannin kasar Massar,bangarori biyu sun dauka cewa kamata ya yi a karfafa hadin kai dake tsakanin Sin da Massar wajen manyan ayyuka da yawon shakatawa da zuba jari da sadarwa,da gina sashen musamman na bunkasa tattalin arziki a Suez Gulf dake arewa maso yammacin kasar Massar da yin sauran ayyukan hadin kai da ake yi da za su iya ba da jagora da taimako a kasar Massar.Mr Wu Bangguo da takwaransa na Massar sun sa hannu kan wata takardar fahintar juna game da kafa wani shirin yin mu'amala cikin lokaci lokaci tsakanin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da majalisar jama'a ta Massar,ta haka aka tabbatar da mu'amala tsakanin majalisun na kasashen Sin da Massar bisa tsare tsaren da aka shirya.

Duk lokacin da majalisar ta kasar Sin ke tattaunawa da majalisun na kasashen uku,bangarorin biyu sun bayyana cewa za su kara mu'amala da hadin kai tsakanin kwamitoci na musamman da tawagogin sada zumunta tare da nufin bunkasa dangantaka ta tsakanin kasa da kasa da kuma daukaka cigaban ziyarar juna tsakanin manyan jami'an kasashen,da musayar fasahohi wajen shimfida yanayin demokradiya da dokoki da tafiyar da harkokin mulki,da kara fhimtar juna da dankon zumuncin dake tsakanin jama'ar kasashen ta mu'amala tsakanin majalisun da kuma kara amincewar juna a fanin siyasa da bunkasa hadin kai mai amfani a fannin mu'amalar tattalin arziki da ciniki da al'adu da kanana hukumomi da kuma kara wani bakon abu wajen bunkasa dangantaka tsakanin kasa da kasa a dukkan fannoni ta yadda za ta samu sabon cigaba.

Jama'a masu sauraro,wannan dai ya kawo karshen shirinmu na yau na Duniya Ina Labari.Mun gode muku saboda kuka saurarenmu.