Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-26 18:35:41    
Kwamitin sulhu na M.D.D. ya kalubalanci kasar Sudan da ta aiwatar da shirin ba da taimako ga rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta AU da M.D.D. ta kaddamar a duk fannoni

cri
Jiya 25 ga wata, kwamitin sulhu na M.D.D. ya bayar da sanarwar shugaba, inda ya kalubalanci gwamnatin Sudan da ta aiwatar da shirin ba da taimako a duk fannoni da M.D.D. ta kaddamar domin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta AU da ke shiyyar Darfur, ta yadda za a girka rundunar sojojin hadin gwiwar M.D.D. da AU tun da wuri.

Sanarwar ta nuna maraba ga cimma daidaito bisa mataki na farko da babban sakataren M.D.D. Ban Ki-Moon da shugaban kwamitin kungiyar AU Alpha Oumar Konare suka yi wajen aika da rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta hadin gwiwar M.D.D. da AU, sanarwar ta ce, wannan shi ne muhimmin matakin da aka dauka domin warware maganar shiyyar Darfur a dukan fannoni.

Bayan haka kuma sanarwar ta yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa, da su nuna goyon baya ga kokarin da ake yi domin warware matsalar shiyyar Darfur ta hanyar siyasa, da kuma nan da nan su dakatar da ayyukan kai farmaki kan farar hula da masu wanzar da zaman lafiya, ta yadda za a tabbatar da aikin aiwatar da ayyukan ba da taimakon jin kai. (Bilkisu)