Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-26 18:25:10    
MDD ta yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Suda ke yi domin daidaita matsalar Darfur

cri

A ran 25 ga wata a birnin Geneve, kungiyar da ke kunshe da kwararru masu zaman kansu na majalisar hakkin 'dan Adam ta MDD ta gama taro na kwanaki biyu da suka gabata, wanda ta shirya tare da tawagar wakilai ta gwamnatin kasar Sudan, kungiyar kwararrun ta yaba wa kokarin da gwamnatin kasar Sudan take yi domin daidaita matsalar Darfur.

Kwararrun sun nuna maraba ga matakan da gwamnatin kasar Sudan ta dauka na yarda da girke sojojin kawance na MDD da kungiyar AU, kwararrun suna ganin cewa, wannan aiki zai ba da taimako ga kyautatuwar halin Darfur. Kungiyar kwararru da tawagar wakilai ta kasar Sudan sun tabbatar da cikakkun matakai da za a dauka game da yadda za a aiwatar kudurin MDD.(Danladi)