Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-25 13:00:33    
Beijing na kokarin daidaita alamun da ake rubutawa a wurare daban-daban na birnin cikin Turanci domin taron wasannin Olympic

cri

Aminai masu sauraro, ko kuna sane da cewa, sunan babban titi na Wangfujing, wani shahararren titin kasuwanci na birnin Beijing shi ne ' Wangfujing Dajie' ko ' Wangfujing Street' ? kuma sunan babban Jami'ar Qinghua shi ne ' Tsinghua University' ko ' Qinghua University' ? Lallai wadannan maganganu guda biyu sukan kawo cikas ga masu yawon shakatawa masu tarin yawa daga kasashen waje wadanda suka zo nan kasar Sin domin yin balaguro. Amma, kada a damu domin za a warware wadannan maganganu kafin shekara mai zuwa.

Mr. Peter Raymond, wani dan Canad dake aiki a nan kasar Sin ya fada wa wakilinmu wani abun ba da dariya da ya auku yau da shekaru guda da ta gabata yayin da ya zo nan birnin Beijing a karo na farko tare da wani amininsa daga kasar Amurka. Mr. Raymond ya ce, kwana na biyu bayan da amininsa ya iso nan Beijing, yana so ya dauki jirgin kasa dake tafiya a karkashin kasa wato subway zuwa babban titi na Wangfujing domin yin yawo. Da ya sauka daga jirgin, sai ya ga alamun da ake rubutawa cikin harshen Turanci a cikin babban dakin subway a kan cewa "Wangfujing Street", sai ya yi tsammanin cewa lallai babban titi na Wangfujing ba nisa; Amma da ya fito daga ginin subway, sai ya ga alamun da ake rubutawa cikin harshen Sinanci a kan cewa ' Wangfujing Dajie'. Nan take Mr. Raymond ya yi mamaki yana dariya. Ya ce, ashe Wangfujing ya bace! Yanzu, Mr. Raymond ya rigaya ya zama mai aikin sa kai na harkar daidaita alamun da ake rubutawa cikin harshen Sinanci da na Turanci. Kuma aminansa masu yawa daga ketare su ma sun shiga cikin wannan harka.

Ko shakka babu rashin daidaitawar rubutun alamun harshen Sinanci da na Turanci ya kawo cikas ga aminai baki. A idon Sinawa, "Wangfujing Dajie" wani wuri ne; Amma a idon aminai baki, " Wangfujing Dajie" da " Wangfujing Street" wurare guda biyu ne daban-daban. A shekara mai zuwa, a nan birnin Beijing, za a gudanar da gagarumin taron wasannin Olympic na 29 da na nakasassu na 13 na duniya. A lokacin, 'yan kallo baki da kuma masu yawon shakatawa daga ketare za su taru gu daya a nan birnin Beijing domin kallon gasanni masu ban sha'awa. To, kara daidaita alamun da ake rubutawa cikin harshen Sinanci da na Turanci a wuraren bainal jama'a na birnin zai samar da sauki ga zaman aminai baki a nan birnin Beijing; haka kuma ya zama dole ne ga mayar da birnin Beijig don ya zama wani babban birni na zamani na duniya.

An labarta, cewa a ran 11 ga watan Afrilu, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya shirya taron watsa labarai game da aikin daidaita alamun da ake rubutawa cikin harshen Turanci a wuraren bainal jama'a, inda ya kaddamar da " ma'aunin daidaita alamun da ake rubutawa cikin harshen Turanci a wuraren bainal jama'a ". Mr. Liu Yang, daraktan ofishin kwamitin shirya koyon harsunan waje domin mazauna birnin Beijing ya yi jawabi a gun taron ,cewa tun daga shekarar bara ne aka soma daidaita alamun da ake rubutawa cikin harshen Turanci a wuraren bainal jama'a. An kafa wata kungiyar mashawarta dake kunshe da masana 35 mai kula da aikin fassarawa cikin harshen Turanci.

Sa'annan Mr. Liu Yang ya fadi, cewa a shekarar bara, kwamitin shirya koyon harsunan waje ya yi hadin gwiwa tare da sassan da abun ya shafa don kaddamar da ma'aunin fassarawa cikin harshen Turanci a wuraren bainal jama'a. An kasa ma'aunin cikin kashi shida, wadanda suka hada da fannin gabatarwa, da zirga-zirga, da wuraren yawon shakatawa, da sana'o'in hidimomi na kasuwanci, da filaye da dakunan wasannin motsa jiki da kuma na aikin jiyya da tsabta.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar bara, an rigaya an canza dukkan alamu da yawansu ya kai 6,530 da ake rubutawa cikin harshen Turanci, wadanda aka kafa a kan hanyoyin mota na cibiyar birnin. Yanzu, ana kuma yin wannan aiki a muhimman wuraren yawon shakatawa, da manyan kantuna, da gidajen baje-koli, da dakunan nune-nune, da muhimman wuraren al'adu, da tashoshin subway da bas-bas da kuma na taxi, da hukumomin jiyya da tsabta, da filaye da dakunan wasannin motsa jiki da kuma wuraren kiyaye muhalli da dai sauransu na birnin Beijing.

An tabbartar da, cewa za a kammala wanna aiki ne kafin karshen shekarar da muke ciki. A karshe dai, Mr. Liu ya yi kyakkyawan fatan alherin cewa, a lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekara mai zuwa, 'yan wasa, da masu koyar da 'yan wasa da kuma masu yawon shakatawa daga kasashe daban-daban na duniya za su iya gano babban titi na Wangfujing na Beijing cikin sauki tare da sakin jiki.(Sani Wang)