A ran 24 ga wata, kakakin MDD Marie Okabe ta bayyana cewa, MDD da kungiyar tarayyar Afirka wato AU sun riga sun daddale yarjejeniyar farko kan batun jibge sojojin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa a shiyyar Darfur ta kasar Sudan.
Kuma Mr. Okabe ta ce, bayan da babban sakataren MDD Ban Ki-Moon da shugaban kwamitin kungiyar AU Alpha Konare suka yi shawarwari tsakaninsu, sun daddale wannan yarjejeniya. Haka kuma Mr. Ban ya riga ya gabatar da kan batun ga Zalmay Khalilzad, shugaban kwamitin sulhu na MDD na wannan wata kuma zaunannen wakilin kasar Amurka a MDD.
Mr. Khalilzad ya zanta da manema labarai, cewa kwamitin sulhu zai kira taro a ran nan da yamma domin tattaunawa kan rahoton da Mr. Ban ya gabatar, kuma mai yiyuwa ne za a zartas da wata sanarwar shugaba kan batun a ran 25 ga wata.(Kande Gao)
|